Man fetur da ake sha a Najeriya ya ragu da kashi 35


Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA ta ce yawan man da ake amfani da shi a ƙasar a kowacce rana ya ragu zuwa lita miliyan 46.34, sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi. Shugaban hukumar, Ahmed Farouk, ne ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan harkokin albarkatun man fetur da iskar gas a birnin Legas, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya ruwaito.Ya ƙara da cewa raguwar ta kai kashi 35 cikin 100 idan aka kwatanta da lita miliyan 65 da ake amfani da shi a kowacce rana kafin cire tallafin man fetur ɗin. Ahamed Farouk ya ce ''a watan Janairu fabrairu, an sha mai lita miliyan 62 a kowacce rana, yayin da aka sha lita miliyan 71.4 a kowace rana cikin watan Maris, sai Afiru da aka sha lita miliyan 67.7 a kowacce rana, sai watan Mayu da aka sha lita miliyan 49.5 a kowace rana, sai kuma watan Yuli da ake shan lita miliyan 46.3 a kowace rana''.

Shugaban hukumar ya kuma gode wa 'yan kasuwar da suka nuna sha'awarsu wajen shigar da man fetur ƙasar daga kasuwannin duniya. Ya kara da cewa kawo yanzu kamfanoni 56 ne suka nuna sha'awarsu wajen shigo da man fetr zuwa ƙasar, yayin da kamfanoni 10 suka zaku wajen fara shigo da man. Ahmed Farouk ya ce yanzu haka kamfanoni uku sun fara shigo da man fetur ɗin daga ƙasashen waje.

Real Naseer Umar Alhassan MNNU 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post