A hukumance, Gwamnatin kasar Iraqi ta nemi jakadiyar kasar Sweden da ta gaggauta kwashe nata-ya-nata ta bar kasar ta Iraqi, kuma ta kira Jakadanta da ke a Stolkhom ta Sweden da cewa ya dawo gida a matsayin martani akan ta'addancin da aka yi na kona Alqur'ani mai tsarki a babban birnin kasar.
Kamar yada ya zo a cikin bayanin shine cewa: "Firaministan kasar Iraqi, Sayyid Muhammad Shiya' Sudanee ya bada umarni ga Ma'aikatar harkokin wajen kasar da ta gaggauta dawoda Jakadan kasar da ke a birnin Stockholm na Sweden zuwa gida.
Haka zalika ya kara da cewa, Firaministan ya kuma umarci jakadiyar kasar Sweden da ke zaune a birnin Bagadaza da ta gaggauta barin birnin ba da bata lokaciba, a matsayin raddi ga kona Alqur'ani da aka yi a kasar Sweden tare da goyon bayan mahukuntan kasar ta Sweden.
Baban Humaid Mnnu/Ng0027 Ma'asumah Nigerian News Update