Kuri'arka 'Yancinka in ji Miyagun Malaman addini a Nigeria.
Wannan maganar ta kuri'arka 'Yancinka Shi aka rinka fadawa talakawan Nigeria a wuraren daurin aure, wuraren radin suna, wuraren wa'azi, kasuwanni, tashoshin mota har da makabarta.
Cewa ake yi wai idan baka kada kuri'a ba baka da 'Yanci, kuma baka da ikon yin magana baka cika dan kasa nagari ba.
Idanko ka kada kuri'arka to zaka zabi Shugabanni nagari, masu gaskiya, rikon amana da adalci.
Wadannan maganganun su zaka ji a Masallatan unguwanni kauyuka da birane, su zakaji ana fada a Gidajen Rediyon Nigeria da Talabijin ballantana uwa uba social media.
Tambayar da zamu yiwa Wadannan mutanen sune:
Yaushe kuri'a zata fara yiwa talakawa amfani?
Yaushe talakawan Nigeria zasu samu magunguna a Asibitocin Nigeria dalilin kuri'a ?
Yaushe kuri'a zata inganta makarantun Primary, Secondary da Manyan makarantu?
Yaushe kuri'a zata samarwa al'ummar Nigeria hanyoyin mota, ruwan famfo, wutar lantarki da abu mafi muhimmanci wato tsaro?
Yaushe kuri'a zata samarwa al'ummar Nigeria ingataccen tsari na walwala da jin dadi a matsayinsu na 'Yan-kasa?
Shin talakawan da suka yi zabe ne suke cin moriyar kuri'a ko kuwa wadanda suka zama Shugabanni da kuri'ar talakawan?
Umar Hassan Gololo
Baban Humaid Mnnu/Ng0027
Ma'asumah Nigerian News Update