HATTARA DAI MATA AURE BA RA'AYI BANE BAUTAR ALLAH NE"


Da yawan wasu ƴan mata sun ɗauki aure a matsayin

tamkar wani abun gasa ne wanda in wance bata yi ba, to

shi kenan an sami abun yi mata gori"

-

"Wasu ƴan matan kuma za suyi aure, amma basu san

darajar auren ba, za ka ga suna raina matsayin aurensu,

sukan ji tamkar su ba matan aure bane sabida da basu yi

ilmin auren ba"

-

"Wasu kuma sun san cewa haƙiƙa aure bauta ne a garesu,

sabida haka su sun zo yin bauta ne gidan mijinsu, kuma sun

san cewa haƙiƙa sun sami ƴanci fiye da wanda suke dashi

a gidajen iyayensu"

-

"Aure ƴanci ne a gareki, kiyi ƙoƙari ki zauna a gidan mijinki

koda kuna da yawa a gurinsa, ki zamto mai biyayyar aure,

kada ki zamto mai wulaƙanta zamantakewar aure. 


Da yawan ƴan mata a waje suna son su taka irin matsayin da kika taka na yin aure, amma basu sami dama ba, to ke da kike da auren kiyi ƙoƙari ki riƙe kayanki ta hanyar yin gaskiya da

adalci da kuma kyautata dukkanin haƙƙoƙin mijinki shine auren"


Baban Humaid' Ma'asumah Nigerian News Update, Mnnu/Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post