Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutum 8 A Najeriya


 Akalla mutum takwas ne suka mutu bayan da wata motar dakon mai ta fashe a yankin kudu maso yammacin Najeriya yayin da mazauna yankin su kuma ke ta kokarin kwashe mai daga tankar, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a ranar Litinin. WASHINGTON, D.C. - Tankar man ta yi hatsari ne a daren Lahadi a wata unguwa da ke jihar Ondo, lamarin da ya yi sanadin da ta kaucewa hanya ta kuma kife, in ji rundunar ‘yan sandan

“Wasu mutane sun je wajen don kwasar mai daga tankar, amma ana cikin haka ne sai motar man ta fashe,” in ji kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, Fumilayo Odunlami-Omisanya. Farashin man fetur a Najeriya ya ninka fiye da sau uku tun bayan da aka cire tallafin wanda aka kwashe shekaru aru-aru ana amfani da shi. Lamarin ya shafi masu ababen hawa da gidaje da kananan ‘yan kasuwa masu amfani da injinan man fetur wajen samar da wutar lantarki.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post