Shekaru 9 da waki'ar Kudus: an yi taron tunawa da shahidai 34 da aka kashe
Kamar yadda aka saba a duk shekara, Harkar Musulunci a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na gudanar da taron tunawa da waki'ar Kudus wacce ta auku a ranar 25 ga watan Yulin 2014 a garin Zariya, a bana ma ba su yi kasa a guiwa ba, inda suka gabatar da taron.
Taron na bana kamar koyaushe ya gudana ne a muhallin Darur Rahma dake garin Zariya. An soma ne da misalin karfe 8 na safe da saukar Alkur'ani mai girma wanda Madrasat Darur Imam Mahdi (A.F). Sannan aka bude taron da addu'a wanda Malam Musa Tudun Jukun ya yi, sannan Mahdi Salihu Garba ya karanto ayoyi daga Alkur'ani mai girma.
An bai wa Ittihadus Shu'ara dama suka haskaka wurin da wakokin juyayi na munasabar waki'ar Kudus. Daga nan Mu'assasoshi, dandamaloli, da Rijal daban-daban da suka hada da; Hurras, Intizarul Imam Mahdi, Kasshafatul Imam Mahdi, Jaishi Aliyul Akbar, Ansaru Zakzaky, Rijalu Zakzaky, Harisawa 'yan Orientation, Rijalu Sidi Zakzaky, Fa'iz Club, duk sun gudanar da 'display' da kareti, takwaendo da kuma faretin girmamawa ga shahidan.
Daga nan I.M Productions suka gudanar da Tamsiliyyah dangane da yadda waki'ar ta auku inda Tamsiliyyar ta shiga zukatan mutane tare da shiga alhini da juyayi.
Sayyid Badamasi Yaqoub shi ne mai jawabi na farko a yayin taron. Inda ya ce ma'anar 'La'ilaha illallah Muhammadur Rasulillah' tana dauke da jarabawa, ya ce duk wanda ya rike wannan kalma gam yana aiki da ita, dole ne fir'aunonin zamani su yake shi kuma ba za su kyale shi ba. Domin a cewar Malamin kalmar na koyar da bara'a da wulaya ne.
Ya ce shahidan Kudus su sun yi nasara, domin sun yi kyakkyawan karshe an kashe su bisa wannan kalma. Inda ya yi addu'ar Allah yasa suma su yi kyakkyawan karshe irin ma shahidan Kudus.
Bayan kammala jawabinsa, an sanya jawabin Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na tunawa da wannan rana. A cikin jawabinsa, Shaikh Zakzaky ya kawo yadda makiya a koyaushe .
Baban Humaid Ma'asumah Nigerian News Update. Mnnu//Ng0027