Gwanda kamar yanda muka sani, a na kiranta ga dukkanin
Hausar Arewacin Nigeria,bishiya ce dake da tsayi wacce
take da ganye launin kore(green leaves),tana haifuwar ‘ya’ya
manya wadanda keda zaki amma kuma zakin nasu bana
sukari bane,natural sugar ne a tare da su.Ya’yan gwanda
waton (fruits) suna kumshe da dimbin sinadirrai masu
matukar amfanar jiki (essential vitamins and minerals )
Ganyen gwanda na ha6aka garkuwar jikin dan adam.Su dai
garkuwar jiki waton (immunity) sune ke zama a matsayin
sojojin dake yaki da abokan gaba waton suna yaki da
kwayoyin cuta a jiki,dan haka idan suka karamta ko su kayi
rauni to a hakika jikin dan adam zai raggwanta kuma zai iya
fuskantar barazanar kamuwa da cutuka daban daban.A dalili
da haka akoi bukatar jikin dan adam ya samu garkuwar jiki
masu karfin gaske dan su iya baiwa jiki kariya daga abokan
gaba.Domin samun wannan damar to sai a lazimci amfani
da tsirran itatuwan da kimiyya ta bada tabbacin cewa suna
boosting na immunity ciki harda gwanda.