Goba bishiya ce da ta samo asali daga yankin kudancin da tsakiyar nahiyar Amurka.
‘Yayanta da ganyenta na da amfani da dama ga lafiyar dan’adam.
Mun tattauna da likita, Usman Bashir a kan alfanunta.
1 - Tana dauke da sanadaran gina jiki na bitamin C da bitamin A. Wannan zai samar da dandanon sukari a abin sha kuma za su iya samar wa dan’adam da kuzari.
2 - Kare lafiyar jiki: Goba na dauke da sanadarai masu wanke abubuwan da ke iya cutar da dan’adam a cikin jiki.
3 - Wanke ciki: ‘Yayan goba na dauke da abin da ake kira ‘fiber’ wanda ke taimakawa wajen wanke ciki da fitar ba-haya.
4 - Rage damuwa: Masanin ya ce kamshin goba na rage damuwa a lokacin da dan’adam ya shake shi.
5 - Samar da inuwa: Bishiyar goba na samar da inuwa ga dan’adam musamman a yankuna masu yanayin zafi na rana.
Real Naseer Umar Alhassan