27 JULY RANAR DA BATURE YA KASHE MUSULMI A BORMI, YA ƘONA ALKUR'ANI, YA SAUƘE TUTAR MUSULUNCI YA ƊAURA TUTAR SARAUNIYAR INGILA

 



__Sheikh Ibraheem Zakzaky [H]

..Garin bormi, a nan Bature ya cimma Sarki Attahiru da jama’arsa waɗanda ba su yarda su mika wuya ga bature da tsarin da ya zo da shi ba, ya kashe su. Bature ya kona Alkur’ani, ya sauke tutar Musulunci da Shehu Dan Fodiye ya kafa ta, ya dora tutar sarauniyar Ingila! “Bature ya kashe Sarkin Musulmi Attahiru ne don ya nuna cewa ya ci kasar nan da yaki, saboda a lokacin (da ya kashe Sarki Attahiru din) ba shi da bukatar ya yi wannan yakin na shisshigi, domin shi Attahiru ya bar Sokoto ne da nufin ya fita ya barta, ba wai ya fito ne da nufin zai je ya yaki Bature ba. Ya yi nufin ya fice daga Sokoto ne (ya tafi wani wajen) da ransa.” Saboda karfin da suka saka a kansa da nufin ganin bayansa.


  “Amma sai Turawa suka saka tsaro a dukkan hanyoyi, cewa duk wanda aka gani ko ake tsammanin cewa shi (Sarki Attahiru) ne, a kama shi a kawo shi da ransa. Har ma sun kakkama wasu, in sun fahimci suna son su je su riski Attahiru ne sai su kashe su. To, kuma mutane daban-daban daga garuruwansu duk sun rika fita suna cimma Attahiru. Har ya zama jama’a masu yawa suka zo tare da shi.”


 “Attahiru da Jama’arsa, sun doru ne a kan wani bayani da aka musu na abin da zai zo nan gaba, an basu labarin zuwan Nasara, an kuma ba da labar cewa tudun mun-tsira idan (Nasara ya shigo kasar nan) kawai sune Tuddan Bima. Saboda haka hankoron Sarki Attahiru (bayan ya baro Sokoto a wancan lokacin) shine ya isa Tuddan Bima din. To kuma sun isa Tuddan Bima din, amma sai ya zama shi Bature ma ya isa, har ya harba Igwa, saboda haka suka bar Bima suka dawo Bormi, to kuma sai Bature ya iso nan Bormi din ya aikata abin da ya aikata.”


_Sheikh Zakzaky (H] Cikin Jawabinsa kan yadda Turawan Mulkin Mallaka suka shigo kasar nan. 2013


@Szakzaky's Gallery' 27/7/2023

Dan Fudiyya Gumau 📝📝📝 

Baban Humaid Ma'asumah Nigerian News Update. Mnnu//Ng0027


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post