YAƘIN BADAR, BABBAN YAƘI NA FARKO A MUSLUNCI




©️ Abdulhadi Aminu.


A rana mai kamar ta yau 17 ga watan Ramadan shekara ta 2 bayan hijira yaƙin Badar ya auku.


Yaƙin Badar shi ne yaƙin farko da musulmi suka yi da mushrikan ƙuraishawa bayan hijira zuwa Madina, wanda ya kasance ƙarƙashin jagorancin Manzon Allah (SAWW), yaƙin dai ya faru ne a ranar 17 ga watan Ramadan shekara ta biyu da hijira a yankin Badar.

A cikin wannan yaƙin dmusulmi sun yi galaba a kan abokan adawarsu, wannan nasara ta ƙara ɗaukaka matsayin musulmi a Madina.


INA NE BADAR?


Yankin Badar yana kudu maso yammacin garin Madina da tazarar kilomita 153, kuma yana arewacin Makkah Al-Mukarramah kimanin kilomita 300 daga gare shi. 

Birnin Badar a yau yana tsakiyar Wadi Al-Safra kuma yana kan mararrabar tsakanin Makkah Al-Mukarramah da Jeddah da Yanbu, kuma ta nan ne tsohuwar hanyar Madina ta bi, kuma yanki ne mai muhimmanci ga matafiya zuwa arewacin Hijaz.


DALILIN YAƘIN BADAR.


Kafin hijirar Manzo s.a.w.w musulmi sun fuskanci zalunci iri-iri da cutarwa da azabtarwa da kora daga mushrikai, har an hana su gudanar da aikin Hajji, duk da haka Allah Madaukakin Sarki ya kasance yana umartar musulmi da su yi haƙuri, don haka musulmi suka himmatu wajen samar da natsuwa da aminci a rayuwarsu, amma bayan hijira sai Allah Maɗaukakin Sarki Ya saukar da ayoyi wanda a cikinsu ya lissafta zaluncin da aka yi wa musulmi ya kuma ba su izinin yin yaƙi, daga cikinsu akwai abin da ya zo a cikin suratul Hajji:


"أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَاتَلُونَ بِأَنَّهُمْ ظُلِمُوا وَإِنَّ اللَّهَ عَلَى نَصْرِهِمْ لَقَدِيرٌ"

"An yi izini ga wanda ake yaƙa cewa an zalunce su, kuma haƙiƙa Allah mai iko ne a kan taimakon su"


Kafin yaƙin Badar musulmi sun yi ƙananun yaƙoƙi da dama ta hanyar hana fataekn ƙuraishawa giftawa ta Madina da iyakokinta, manufar ita ce karya ƙashin bayan ƙuraishawa da sarrafa ayarin fatakensu, duk da cewa sau ɗay Musulmi suka yi nasarar kama ayarin ƙuraishawa.


Akwai wata tawagar da Abu Sufyan ya jagoranta zuwa Gazza domin fatauci, sai musulmi suka nufi wannan tawagar amma basu samu nasarar cimma tawagar ba, a lokacin da Abu Sufyan ya samu labari sai ya aika wa larabawa a kan su shirya su fito yaƙi.


Lokacin dawowar wannan tawagar ta Abu Sufyan ne yaƙin Badar ya afku.


YA AKA GUDANAR DA YAƘIN BADAR?


Kafin a fara yakin, Manzon Allah (saww) ya aiko da saƙo ga ƙuraishawa yana sanar da su cewa ba ya son yaƙi, ya kuma gargaɗr su a kan yakin, hakan ya sa wasu mushrikai irin su Hakim bin Hizam suka nemi a koma Makka, amma tsananin girman kai na Abu Jahal ya hana su dawowa tare da cijewa a kan sai an yi yaƙin.


A al'ada ta larabawa ana fara gabatar da karon-batta tsakanin jarumai, abin da suke kira "Mubaraza", dan haka sai Abu Jahl ya ingiza Utba a kan ya fita a ƙwama da shi, a lokacin Utba ya fita tare da ɗansa Walid da kuma Shaiba.


Manzo (SAWW) ya fito da baffansa Hamza, da Ubaida da Imam Ali a.s. inda suka kara kuma suka yi nasarar kashe Utba da Walid da Shaiba, daga nan yaƙi ya ɓarke.


Yaƙin Badar ya ƙare ne da shahadar musulmi 14 (Shahidai 6 daga Muhajirai da Ansaru 8) da kuma mutuwar mushrikai 70 tare da kama 70, sauran kuma suka shige cikin daji domin gudun tsira da ransu.


Imam Ali a.s shi ne jarumin ranar Badar, wanda a mafi ƙarancin riwaya ya kashe mutum 21 a cikin waɗannan mushrikai 70 shi kaɗai.


Yaƙin Badar bai yi tsawo ba kamar sauran yaƙoƙi a tarihin musulunci, inda bai wuce rabin yini ba aka kammala yaƙin.


BAYAN KAMMALA YAƘI.


A ɓangaren musulmi, bisa umarnin Manzon Allah (SAWW) an tara dukiyoyi da ganima a wuri guda, aka binne shahidan musulmi aka raba ganima, su kuma gawarwakin mushrikai aka tara su waje ɗaya a rami ɗaya.


A makka kuma Abu Sufyan ya hana a yi zaman makoki domin wutar ɗaukar fansa ta ci gaba da wanzuwa a zukatan mutane, an yi wata ɗaya a Makka na baƙin ciki da kuka.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post