Kamar yadda aka ayyana yau Asabar 1 ga watan Aprilu 2023 ne yan uwa musulmai almajiran Sheikh Zakzaky zasu karbi ababan hawansu motoci mashina Keke Napep. Wanda jami'an tsaro suka kwashe wani ba 'adi agidan sheikh Zakzaky gyallesu , dakuma Husainiyya Bakiyyatullah a shekarar 2015 bayan kisan dubban yan uwan a zariya.
Yan uwan dai sun hallara police station dake MTD Zariya inda bayan tantacewa kowa yafara daukan nashi. Saidai yan uwan sunyi korafin dayawansu sun rasa wasu sassan na Motocin nasu cikin abubuwan dasuka bata harda inji nawasu motocin.
Ababan hawan dai da aka bayar yau motoci guda 67 mashina karfe karfe guda 10 , Keke Nafef guda 3. sa'ilin da ninkin adadin abin hawan anyi wasoso .wasu kuma ankona , wasuma agaban masushi ake saidawa .
Ayau da'ake karban ababan hawan , dayawa daga cikin masushi suna cikin wanda aka kashe agyallesu gidan sheikh Zakzaky ko kuma Husainiyyan.
Tags:
Daga marubata