WAYE IMAM HASAN ƊAN ALI ƊAN ABI ƊALIB (AS) ??



Imam Hasan shi da ne ga Imam Ali ɗan Abi Dalib ɗan Faɗima yar Annabi Muhammad (saww), kuma shine farkon wanda aka fara sanyawa wannan sunan, Manzon Allah shine ya raɗa masa suna.

 


An haifi Imam Hasan (as) a daren talata ranar (15) ga watan Ramadan, ashekara ta uku (3) bayan hijirar Annabi (sww) a madinatul munawwara.


Ya kasance Ana yi masa lakubba Kala Kala, daga ciki a kwai


1- Almujtaba

2- Azzakiy 

3- Alwaliy

4- Assibɗul Akbar 

5- sayyudu shababi Ahlil Jannah 

6- As Sayyid 


Sannan Ana masa Alkunya da Abu Muhammad.


Imam Hasan (a.s) ya kasance yana da 'ya'ya goma sha Biyar, guda takwas Mata guda bakwai Maza. 


Imam Hasan (as) ya rayu a duniya tsawon shekaru (47) a wata ruwayar kuma shekara (48),

Ya rayu da kakansa Manzon Allah tsawon shekaru bakwai da ƴan watanni, ya kuma rayu da babansa Imam Ali (as) tsawon shekaru talatin da bakwai (37) bayan shahadar Abbansa ya rayu shekara goma kafin shahadarsa.

 

 

Imam Hasan (as) yafara Imamanci a ranar (21) ga watan Ramadan a shekara ta (40) bayan hijira yacigaba da Imamanci har   zuwa ranar  (28) ga watan Safar shekara ta (50) bayan hijira kenan yayi shekara goma yana Imamanci amincin Allah ya tabbata agareshi.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post