Asalin tanajin da aka tanada don Imam Hasan (a.s.) ya
tabbatarwa samuwarsa ta ruhi wata kololuwar daukaka.
Kusancinsa ga Allah da ta’allakursa da Shi wani al’amari
ne da ke girgiza zuciya kuma hankali ke mika wuya a kai.
Imam al-Sadik (a.s.) yana cewa:
“ Imam Hasan bin Ali ya kasance mafi bautan mutanen
zamaninsa, kuma ya fi su gudun duniya da daraja ”.
Haka nan ya zo cikin littafin Raudhatul-Wa’izina cewa:
“(Imam Hasan) Ya kasance idan yana alwala sai jikinsa ya
rika kakkarwa kuma launinsa ya canza, da aka tambaye shi
dalilin haka sai ya ce:
“ Hakki ne aka duk wanda ya tsaya a gaban Ubangijin
Al’arshi launinsa ya canza kuma gababunsa su kada ”.
Ya kasance idan ya isa kofar Masallaci ya kan daga kansa
ya ce:
“Ya Allah! BakonKa ke kofarKa. Ya Mai yawan kyautatawa
hakika, mai munanawa ya zo maKa, to Ka ketare munanan
abubuwan da ke gare ni da kyawawan abubuwan da ke
gare Ka, Ya Ma’abucin karimci ”.
Ya kasance idan yana karanta Alkur’ani, duk lokaci da ya
zo ayar da da ke cewa: (Ya ku wadanda suka ba da
gaskiya ) yakan ce: “ AmsawarKa! AmsawarKa!! Amsa-
warKa!!!
An ruwaito daga Imam al-Sadik (a.s.) cewa:
“ Imam Hasan bin Ali (a.s.) ya tafi hajji har sau 25 da kafa.
Ya kuma raba dukiyarsa biyu ya ba Allah rabi ”.
Kyawawan dabi’unsa kuwa wani abu ne mai misalta
dabi’un Alhlulbaiti (a.s.). Littafan tarihi sun hakaito cewa:
“Imam Hasan ya taba bi ta wajen wasu mutane matalauta,
a lokacin suna tsintar guntattakin gurasa da aka ci aka
rage kuma aka watsar a hanya, suna ci. Da suka gan shi
sai suka yi masa tayin ya zauna ya ci tare da su. Sai kuwa
ya amsa musu da cewa: ‘ Hakika Allah ba Ya son masu
girman kai.’ bayan da ya gama da su sai ya gayyace si
bakuntarsa, sai ya yalwata su da dukiya mai yawa, ya
kuma ciyar da tufatar da su”.
Wata rana an taba ce masa: “Me ya sa ba mu taba ganin
ka ki amsawa mabukacin da ya tambaye ka ba?” sai ya
amsa da cewa:
“ Hakika ni ma mai rokon Allah ne, kuma mai kwadayi gare
Shi; don haka ina kunyar in zama mai roko alhali kuma ina
hana mai roko. Kuma Shi (Allah) Ya sabar da ni da bayar
da ni’imarSa gare ni, haka ni ma na sabar da Shi in bayar
da ni’marSa (da Ya ba ni) ga mutane; to ina tsoron in na
yanke al’adata Shi ma Ya yanke al’adarSa ”.
Haka nan Imam Hasan (a.s.) ya taba sayen wani lambu
daga wasu mutane Ansarawa da kudi dirhami dari hudu,
sai labari ya zo masa cewa (wadanda suka sayar masa
din) sun koma suna bukata daga mutane, sai ya koma
musu da lambun ba tare da ya karbi kudinsa ba.
Wannan kadan ne daga daga siffofinsa (a.s.), kuma wani
bangare ne na matsayinsa tare da daidaikun wannan
al’umma. Dabi’unsa sun kasance mafi tasiri wajen misalta
kyawawan dabi’un Musulunci .
Mnnu//Ng0027
Ma'asumah Nigerian News Update