@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MUTUWA BA A GUJE MATA, SANNAN RARRABA KUMA SHARRI CE
Cikin Khudubar Imam Ali (A.S) ya yi wasiyyah ga al'umma kamar haka:-
" YAA KU MUTANE, KOWA ZAI HADU DA ABINDA YAKE SON KAUCEWA TA HANYAR GUDU, MUTUWA ITA CE WAJEN DA RAYUWA KE TAFIYA. KU GUDU DAGA GARE TA YANA NUFIN KU JE GARE TA NE " kace ita mutuwar nan da kuke guje mata, to, ita mai haduwa da ku ce (ta gaban Ku) ......
" Duk inda kuke mutuwa za ta riske ku (ta bayan ku)....."
(QUR'AN)
TSAHON WANI LOKACI NAYI INA BINCIKEN SIRRIN WANNAN AL'AMARI, AMMA ALLAH BAI BAYYANAR BA FACE 'BOYRWARTA. FAU! FAU!! WANI ILMI NE ABIN TSARKAKEWA, AMMA DANGANE DA WASIYYA TA TA WARSHE A GAME DA UBANGIJI NE, KA DA KU KUSKURA KU HADA BAUTARSA DA WANI (shi kadai yake ba shi da abokin tarayya) .
KUMA GAME DA MANZON ALLAH MUHAMMAD (S.A W.W) KADA KU YI WATSI DA SHI DA KUMA SUNNAR SA, KU YI RIQO DA WADANNAN GINSHIQAI. MUDDIN BA KU RARRABA BA BABU WANI SHARRI DA ZAI SAME KU. KOWA A CIKIN KU SHINE ZAI 'DAUKI NAUYINSA (wajen kawo daidaito da kaucewa rarraba), AN SAUQAQA WANNAN NAUYI AKAN JAHILAI (don su ba a biye musu, in kuwa aka biye musu to, zaman lafiya da hadin kai ba zai taba samuwa ba).
ALLAH MAI RAHMA NE MAI JIN QAI, MANZO (S.A.W.W) KUMA SHI NE MAI RIQE DA ILIMI. JIYA INA TARE DA KU, AMMA YAU NA ZAMA ABIN MISALI A GARE KU, GOBE KUMA ZAN BAR KU. ALLAH YA GAFARTA MIN YA KUMA GAFARTA MUKU !"
(NAHJUL-BALAGHA, SH:299).
😭 😭 😭 😭 😭 😭 😭
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034.
~ 20th November, 2019.