Wasiyyar Imam Aliy (a.s) Ga 'Yar'YAnsa Kafin Shahadar Sa (1)..!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


YA UMARCE SU KAN YIN TSANANI GA AZZALUMAI


Bayan saran da Ibn Muljam (L.A)yayi masa, kuma yaga ba zai rayu daga wannan saran ba,  sai ya kira 'ya'yansa Hassan da Hussaini (A.S) yayi musu wasiyya kamar haka;


‘’ Ina yi muku wasicci da tsoron Allah da kuma shawartaku da kada ku rusana ga (jin dadin )duniya ko da kuwa tana bin ku. Sannan kuma kada kuyi baqin ciki akan wani abu na duniya da aka hana ku. Ku fadi gaskiya da kuma yin aiki don lada, sannan ku kasance masu tsanani ga azzalumai, kuma masu taimakon  wanda aka zalunta.


Ina yi muku wasicci da dukkan 'ya'yayena da iyalaina  da duk wanda rubutuna  ya isa gare shi, da tsoron Allah da tsara al'amranku da kuma kyautata alaqa tsakaninku, don kuwa na ji kakanku (Manzon Allah)yana cewa; ‘’ KYAUTATA TSAKANI YA FI SALLAH DA AZUMI .‘’


Ina hada ku da Allah cikin al'amarin marayu, kada ku bari  su shiga wahala, sannan kada a cutar da su a gabanku.


Ina hada ku da Allah cikin al'amarin maqwabtaka, don kuwa sun kasance wasiyyar Annabinku. Ya kasance yana yawan magana a kansu har sai da muka tsammaci  zai ba su wani  shashe na gado.


Ina hada ku da Allah cikin al'amarin Al-Qur'ani, kada ku bari waninku ya wuce gabanku  wajen aiki da shi.


Ina hada ku da Allah cikin lamarin sallah, don ita ce jigon addininku .‘’


ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.


Daga wakilanmu na Bauchi zone.


Tare da Ado Isah Guda.


         09039791509


~11th May, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post