Tun bayan wafatin Isma'il ɗan Imam Ja'afarus Saadik ɗan Imam Muhammadul Baqir ɗan Imam Ali Zainul Abidin ɗan Imam Hussein ɗan Imam Ali bin Abi Ɗalib (a.s) , Sai wasu daga cikin sahabbansa suka dage kan cewa shi ne Imamin ‘yan Shi’a a bayan mahaifinsa duk da ya rasu a rayuwar mahaifinsa amma suka ce Imamanci a zuriyarsa yake , saboda sun yi imani da cewa bai rasu a zamanin mahaifinsa ba wai Imam Ja’afarus Sadiq ya yi masa jana'izar ƙarya (Wahami) ne don ya kau da idon Abbasiyawa daga gare shi, kuma wai Isma'il ya gudu ya kafa kira a ɓoye shine kaza shine kaza .....
Don haka suna ganin Imamanci ba ya cikin zuriyar dan uwansa Imam Musal Kazim (a.s) , wanda Ijma’in Shi'a Imamiyya ya tabbata a kansa bayan Shahadar Imam Ja’afar (a.s) Imami na Shida kamar yanda yazo daga Annabi (saww) cewa Imamai sha biyu ne , haka kuma Imam Ja'afar (a.s) ya ta nanata Imam Musal Kazim (a.s) ne magajinsa , amma sai suka ce Imamanci na ga Muhammad ɗan Ismail ɗin , wanda ake yi wa Laƙabi da Al-Maktuum kuma shine limaminsu na bakwai daga shi sai Ahmad na takwas daga shi sai Muhammad shine na tara , daga shi sai Az-zakiy shine na goma haka dai suke tafiya da imamai barkatai har zuwa yau ɗinnan .
Isma'iliyya sun ci gaba da aiki cikin sirri da ɓoyewa har zuwa lokacin da yunƙurin Ubaidullah Al-Mahdi ya bayyana a kasar Maroko kuma sai karansu ya isa tsaiko da hakan , sannan a bayansa Al-Mansur ya karɓi Shugabanci , daga shi sai Al-mui'izzu lidinillah Alfaɗimiy , sannan Al-Aziz billah ya karɓeshi sai kuma al-Hakimu bi-Amril llah , sannan al-Zahir, sannan al-Mustansir billah , a bayan wafatin al-Mustansir sai saɓani ya shiga tsakanin ‘ya’yansa biyu, Nizar da Al-Musta'ali.
Al-Musta’li ya samu nasarar karɓe ragamar halifanci da jagoranci da karfin tsiya tare da taimakon kawunsa “Al-Afdal Al-Jamali” kwamandan rundunar Faɗimidiyyawa.
Don haka Isma'ilawa sun kasu kashi biyu daga nan ;
1- Musta'liyya
2- Nizariyya
Su Musta'aliyyawa Jagororinsu sun ci gaba da gudanar da harkokin halifanci a ƙasashen Masar tun a lokacin .
Bayan Al-Musta’li sai Al-Aamir Billah, sai kuma Al-Tayyib bin Al-Aamir, wanda suke da’awar ya shiga cikin kogon ɓuya da fakuwa, a wannan lokacin ne sai mutum huɗu daga cikin wakilan Masarauta da Halifancinsu suka cigaba da gudanar da al'amura , sune :
1- Al-Hafiz.
2- Az-zahir
3- Al Fa'iz
4- Al-Aadhid
A zamanin Al-Aadid ne Salahuddin Al-Ayyubi (L) ya ƙwace iko da al'amuran Daular Fatimiyya don haka ne Isma'ilawa suka watse suka rabu biyu wato Nizariyyawa da Musta'aliyyawa .
Daga nan sai Isma'ilawa a ƙasar Yaman suka kafa ƙungiyar Musta'aliyya Isma'iliyya mai suna "Isma'iliyya Ɗayyibiyya" wanɗanda sune a yau ake kiranta da Mazhabar Buhra.
Ɗayyibiyywa basu wani taka rawa a fagen Siyasa ba , amma sun duƙufa ne kan kasuwanci a tsakanin lardin Indiya da Yamen , lokacin da suka fuskanci matsanancin yanayi da takura a hannun Salahuddin Al-ayyubi suka sami damar yaɗa wannan kira nasu a Indiya, musamman ma a cikin jihar nan ta "Gujrat" da ƴan Addinin Hindu da suka shiga Musulunci sai suka dinga shiga wannan da'awar tasu a can Indiya har suka yi yawan da suke dashi a yau .
Ance asalin kalmar “Bohrah” da ake kiransu da ita an ɗaukota daga"Vehru" wanda ke nufin kasuwanci ko ɗan Kasuwa a yaren Gujarati na Indiya , ana kiransu da hakan saboda mafi yawancinsu kasuwanci ne aikinsu .
A ƙarni na Goma bayan Hijira Ɗayyibiyyawa Isma'iliyya suka ƙara kasuwa kashi biyu zuwa uku , rabe-raben ya samo asali ne sakamakon saɓani a kan wane ne zai karɓi matsayin cikakken mai wa’azin Mazhabar tasu , wanda ake ce masa (الداعي المطلق) wani muƙami ne na jagoranci a cikinsu .
Tawagar farko bayan sun rabu itace: Sulaimaniyah : danganci ne ga mai wa’azi Sulaiman bin Hassan.
Mazhaba ta biyu kuma itace Dawudiyya : Danganci ne ga mai wa’azi Qutb Shah Dawud, mai wa’azi na ashirin da bakwai wanda cibiyarsa ta tashi daga Yaman zuwa Indiya a ƙarni na Goma bayan hijira, kuma mai wa’azinsu shi ne “Tahir Saifud Din”, wanda shi ne mai wa’azi na hamsin da ɗaya a jerin masu wa'azin Isma'iliyya Ɗayyibiyya kuma yana zaune a birnin Mumbai (Bombay) .
Sai kuma Al-Buhratul Alawiyya da suka ɓalle daga Sulaimaniyyawa a 1980 Miladiyya .
Watsewar Isma'ilawa zuwa Musta'aliyya da Nizariyya ana daukarsa mafi girman rabuwa tun kafuwarta a baya har zuwa wannan zamani namu , kamar yadda kowace mazhaba cikinsu ta koma ga limaminta a bayyanarwa kuma ta yi riƙo dashi sannan zuriyarsa a bayansa , sakamakon wannan rabuwar kowace mazhaba tana da nata litattattafai na kanta domin kowace mazhaba tana da masu fafutuka na musamman da masu tsara ilimi da tunaninta , bari ma bayan haka kowace mazhaba tana da mazauninta da Daularta kamar Daular Sulaihiyyawa a Yaman , wacce take wakiltar Musta’liyyawa Isma’ilawa, da kuma Daular Sabbahiyyawa ko Hashashiniyyawa (Mabiya Hasanus Sabbah) da cibiyar su ke Alamut dake Kudancin Farisa wanda su ke wakiltar Isma'iliyya Nizariyya.
Akwai faɗace-faɗace da rikici da mai tsanani da ya shiga tsakaninsu a yankin Farisa , Misra , Yaman , Saudiyya da wani yanki na Sham, amma ba za mu shiga bayanin wannan fagen ba domin shima Karatu ne mai zaman kansa .
Wasu daga cikin al'adu da Aƙidun Buhrawa Isma'iliyyawa da galibinsu suke yawan Ziyartar Haramin Imam Ali da Imam Hussain (a.s) sune :
1.Tufafinsu Maza da Mata na daban ne ta yadda mai lura da idon basira zai gane su da ya gansu dashi , watau farararen tufafi da ƴar hula .
2 . Suna da wuraren ibada na musamman da babu wanda yake shiga sai su , kuma suna kiransa da Masallacin Khanah, kasancewar ba sa yin sallar farilla sai a Masallacin nasu , tare da ƙin yin sallah a masallatan dake mallakar wasu Musulmi sai dai nasu kawai .
Ance ansha ganin Buhiriyyawa suna fitowa daga Masallacin Harami a Makka lokacin Sallah su je su yi Sallarsu daban a wani wurinsu mai suna (Ribaɗus Saif ) da ke kusa da Masallacin Haramin Makka ta can ɓangaren kudu , Allahul Aalim.
3. Suna matukar son ɓoye Aƙidarsu ta Mazhabar Baɗiniyya sosai , a lokaci guda kuma suna yin tarayya da sauran Musulmi wajen aiwatar da wasu ayyukan ibada baki ɗaya .
4 . A wata nahiyar ance suna da taimakon kansu sosai ta fuskar yaƙar talauci a tsakaninsu , kuma ance suna da kuɗi shi yasa shugabanninsu suke da alaƙa da manyan masu faɗa aji na Duniya, Allahul Aalim.
5 . Batun Hadisin Imamai sha biyu a bayan Manzon Allah (saww) suna yi masa tawili su jirkitashi don yayi dai-dai da Aƙidarsu ta Baaɗiniyya da suka ƙirkireta , amma in banda haka Imamai a wajensu ai basu da iyaka .
6. Ance suna ƙin Imam Musal Kazim , Imam Jawad , Imam Aliyul Hadi da Imam Hassan Al-askari (a.s) har suna musu isgilanci.
In hakan ya tabbata wannan ba abun mamaki bane domin dama asalin ƙiyyarsu da faɗansu ya fara da Imam Musal Kazim (a.s) ta yanda suka ƙaryatashi suka yi inkarin Imamancinsa , shi yasa ma ba za ka dinga ganinsu a Kazimiyya (Baghdad ) ba ko Samarra wajen Ziyarar sauran Imaman shiriya huɗu dake Iraƙi , ballantana kuma suke Mashhad, Iran .
7. Basu cika yawo da Takalmi ba a Najaf (Musamman a yankin Harami) wata ƙila girmamawa ko wata Aƙidarsu ce ta sa hakan , Allahul Aalim, kuma dai suna da himmar zuwa ziyara ko da yaushe za ka gamsu a wasu wuraren Ziyara musamman a Najaf da Karbala .
Zancen gaskiya Isma'iliyyawa da Buhrawa da Irinsu Faɗahiyya , Waƙifiyya ba ƴan Shi'a bane ko da kuwa Ahlussunna Wal jama'a suna danganta su ga Shi'a , domin kuwa sunyi inkarin dayawan Imaman shiriya da Annabi yayi bushara dasu , shi kuma yin inkari ko ƙaryata Imami ɗaya a cikin Sha biyun nan tamkar ƙaryatasu ne baki daya , kuma hakan ɓata ne da kaucewa hanya , kuma ba'a lissafa wanda yake da wannan Aƙidar a matsayin ɗan Shi'a cikakke , bari ma wasunsu ba zai yu a lissafa su a cikin Musulmai ba saboda miyagun Aƙidunsu ka Kafirci da Guluwi kamar Ƴan Baɗiniyya da sauransu .
Uwa uba akwai Riwayoyin da suka zo daga Ai'mmatu Ahlil baiti (a.s) suna masu la'anta da Allah wadai da waɗannan mutane saboda Aƙidunsu na ɓata .
Muna roƙon Allah ya tabbatar damu akan tafarkin Annabi da Iyalansa tsarkaka duk rinsti duk wuya kar mu juya baya ko mu saki layi har ƙarshen numfashi .
Wasallamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏
✍️ Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
Sha'aban /1444H - 4/Maris/2023 Miladiyya.