Da farko dai wannan rubutun ba zanyi magana bane kai tsaye akan halascin tashe ko rashin halascinsa a Shari'a , ko inyi batun dacewar abinda ake yi a cikin Tashe yanzu ko rashin dacewarsa , kuma ba wai inaso in bawa al'adar tashe kariya bane , a'a , zanyi magana ne - kamar yanda na rubuta a sama - akan alaƙar Tashe da wafatin Matar Manzon Allah mai girma Sayyida Khadijtul Kubra (a.s) , kamar yanda wasu suke yaɗawa suna cewa ; Wai Tashe ya samo asali tunda Sayyida Khadija matar Manzon Allah (saww) tayi wafati a Ranar Goma ga watan Ramadan , wai wasu maƙiya Annabi (saww) da munafukai suka ƙirkiroshi don yin murna da farin ciki da halin baƙin cikin Annabi (saww) ya shiga bisa wafatimta , suna masu yin isgilanci ga Annabi (saww) suna ce masa gwauro gwauro bashi da mata.... daga nan wai sai manyan Daulolin maƙiya Ahlul baiti (a.s) suka yaɗa shi a cikin Musulmi har yazo ƙasar Hausa kamar dai al'amarin cika ciki da ake yi a ƙasar Hausa .
Dayawan ƴan uwa suna ta tambayata ; Shin hakane ko ba haka bane ? To ga Amsa :
MENENE AL'ADAR TASHE ???
Kalmar tashe dai tana da alaƙa ne da "Tashi" daga barci , kuma masana sunyi bayanin Tarihi da asalinsa suka ce :
Tashe wata al’ada ce ta Hausawa wadda ta samu bayan zuwan Musulunci yankinmu wadda yara (Maza da Mata) da manya maza suke aiwatar da ita a yayin da watan Ramalana in ya kai kwana goma , don nishaɗantarwa , raha , faɗakarwa da tada mutane daga barci .
Kuma makaɗa da maroƙa sukan tayar da mutane ne ta hanyar kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe, sannan bayan azumi sai su bi gida-gida ana ba su abin da ya sawwaƙa .
Akan sami samari majiya ƙarfi da sukan tashi don jin daɗi da nishadi suna ƴan waƙe-waƙe don tayar da jama’a daga bacci a gaf da Suhur .
Kasancewar yara ƙanana musamman ‘yan mata, ba su da damar tashi cikin dare , sai suka shiga wasanni suna kwaikwayon abubuwan da ake yi bayan an sha ruwa haka, sai aka dinga kiran su wasannin Tashe.
Da tafiya tayi nisa , sai ya zamana ba ƙananan yara kaɗai suke yin wasannin tashe ba har da manyan samari waɗanda kan yi ƙungiyoyi suna bi unguwa-unguwa dan gabatar da tashen .
Wannan shine tashen da ake yi a kasar Hausa a taƙaice kamar yanda suka ambata kuma kusan kowa yasan hakan .
TO MENENE ALAƘARSA DA WAFATIN UWAR MUMINAI SAYYIDATUNA KHADIJATU MATAR MANZON ALLAH (A.S) ???
Kamar yanda na faɗa a farko wasu da sukaga cewa a ranar 10 ga watan Ramadan ake fara tashe kuma a ranar ne Sayyida Khadijtul Kubra (a.s) tayi wafati , sai suka ce ai al'adar tashe ta samo asali domin yin murnar Wafatin Sayyida Khadijah ne da maƙiya Annabi (saww) sukeyi tun wancen lokaci , don dai su ƙara ƙuntatawa Annabi (saww) bisa halin rashin matarsa da Baffansa Abu Ɗalib (a.s) da yayi .
A haƙiƙanin gaskiya in muka yi duba (Bayan nazari da bincike ) za mu samu wannan magana bata da wani ingantaccen tushe a tarihance ko a ilmance , ko muce abune mai matuƙar wahaka tabbatar da ita da dalilai ingantattu , ko mu kaishi ga babin zaton da baya gadar da ilmi ko aiki , Hausawa nacewa : Zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya ne !
Ko ba komai in muka kalli tarihin ita wannan al'ada a kasar Hausa dama wasu sassa na Duniya za muga akasin abinda ake yaɗawa yanzu ne , domin kuwa ana yin tashene da wata manufa mai kyau kamar tashin mutane don yin sahur ko don yin nishaɗi da raha .
Kuma maganar gaskiya ba wai iya ƙasar Hausa ba har a wasu ƙasashen Larabawa kamar Iraƙi , Kuwait , Saudiyya , Bahrain da Oman ana yin tashe na yara da manya muna gani.
MISALI :
A ƙasar Iraƙi ana yin Tashe na Manya da suke kiransa Abu Ɗubeilah (أبو طُبيلة) , Saboda yanda matasa manya suke zuwa da Ganguna suna tashin mutane domin yin Sahur , domin a zamanin da ana yin bacci da wuri sai ya zama Hukuma ko mai Unguwa na zaɓar wasu matasa don su dinga bi loko da sako dan tashin mutane , musamman lokacin babu irinsu waya da za'a saita ƙararrawa ga kuma gajiyar ayyuka kuma ba kamar yanzu da ake zama shan Ƙahwa ba , sai ya zama ana kallon abun a matsayin aikin lada saboda tayar da masu Azumi da ake yi suyi Sahur da yake "Mustahabbi" sannan lokcin Idi suna bi gida gida ana basu kuɗi da kyautuka daban daban , ana kiran wannan kyautuka (عيدية) .
Akwai kuma tashe na yara da ake kiransa Majainah (ماجينه) asalinsa daga ما اجينه ne a harshen Iraƙawa ma'anarsa : da bamuzo ba ،, saboda yaran suna fitowa ranar 15 ga watan Ramadan ( Mauludin Imam Hassan a.s.) suna rera waƙa suna cewa :
ما جينه يا ماجينه.... لولا الحسن ماجينه .....حل الكيس وانطينه ، انطونه الله ينطيكم.....بيت مكة يوديكم ....
Ma'ana : Ba don Imam Hassan ba da bamuzo ba , ku zuge bakin jaka ku bamu , ku bamu kuma Allah ya baku , ya kaiku garin Makka ....sai a dinga ɗan basu kuɗi da kyautuka kamar yanda ake a ƙasar Hausa .
In masu gida basu basu fito sun basu komai ba sai su dinga cewa :
يا أهل السطوح
تنطونه لو نروح
Daga baya sai ya zama yaran suna farawa ma tun daga farkon Ramadan har ƙarshe bama iya ranar haihuwar Imam Hassan (a.s) ba , abunka da yaro ya samu abun yi ! Duk da wasu suna kawo wasu ƙossoshin ba wannan ba , amma abinda yake tabbatace shine ana yin tashen Majeinah saboda Mauludin Imam Hassan (a.s) kowa yasan wannan.
Kuma har a ƙasar Kuwait da wasu ƙasashen Larabawa kamar Saudiyya suna yin nasu Tashen suna kiransa da " كركيعان ko قرقيعان" wanda daga kalmar قرقعة ne , ma'ana ƙarar kwanukan da ake zuba ƴan alawowin da ake rabawa yara masu tashe ko kuma ƙwankwasa ƙofar da yaran keyi , a ƙasar Oman suna kiransa da القرنقشوه a Dubai kuma ana kiransa حق الليلة ko حق الله da sauran sunaye mabanbanta a kowanne gari.
A taƙaice dai don fahimtar wannan mas'alar da samun matsaya muna buƙatar mu gane abubuwa kamar haka :
1. Mun san tarihin asalin Tashe a yankunan da ake yinsa ciki har da ƙasar Hausa kuma manufar yinsa a bayyane take har yanzu bamai musa hakan , itace Tayar da mutane daga bacci da kuma nishaɗi da raha , ko ina kaje a Duniya wannan shine Hadafin tashe , duk da lamarin Tashe ya daɗe da taɓarɓarewa sosai , amma da'awar dangantashi da Wafatin Nana Khadija (a.s) babu wani bayyanannen dalili na Tarihi ko ilmi da ya tabbatar da hakan , kusan shaci faɗi ne kawai , domin kowa na iya ƙirƙirar ƙissa yace shine asalin tashe .
2. Don wafatin Nana Khadija (a.s) ya kama 10 ga Watan Ramadhan kuma fara tashe ma a wannan ranar ne baya zama cikakken dalilin da zai tabbatar da alaƙar abubuwan biyu , zai yu ta fuskar kaciɓis ne "صدفة" kamar yanda abubuwa da yawa suna faruwa a haka ba sai mun bada misali ba don kaucewa tsawaitawa , sai kaga don abubuwa mabanbanta sun faru a rana ɗaya da basu da alaƙa sai kawai wasu mutane su samar da alaƙa a tsakaninsu , saboda jahilcinsu ko kuma wata manufa ta musamman ko kuskure, Tarihi cike yake da irin hakan .
3 . Idan kace al'adar tashe na da alaƙa da wafatin Sayyida Khadija (a.s) sai muce maka kuma zai yu yana da alaƙa da murnar haihuwar Imam Hassan (a.s) kamar yanda yara suke yinsa a kasar Iraƙi har suna rera waƙar (لولا الحسن ما جينه) , muma za mu iya cewa daga can ya samo asali yazo mana yankinmu in munaso muyiwa abun kyakkyawar fahimta , kuma mu muna dalili mai ƙarfi akan hakan saɓanin batun wafatin Sayyida Khadija (a.s) da ake faɗa .
4. Cika ciki yana da alaƙa da murnar kashe Imam Hussain (a.s) kuma wannan abu ne tabbatacce har a cikin Littattafan Ahlussunna Wal jama'a - a baya munyi bayanin hakan - amma kuma babu wani ƙwaƙƙwaran dalili akan alaƙar wafatin Sayyida Khadijah da tashen da ake yi a ƙasar Hausa a (Tarihance ko Ilmance ) , illa iyaka batu ne da yafi kama da shaci faɗi ko zato , shi kuma Allah ya faɗa mana a cikin Alkur'ani mai girma :
وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِۦ عِلْمٌ ۚ إِنَّ ٱلسَّمْعَ وَٱلْبَصَرَ وَٱلْفُؤَادَ كُلُّ أُوْلَٰٓئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْـُٔولًا ......
A wata Ayar kuma cewa yayi : Lallai sashin wani zaton zunubi ne .
5. Ga duk wanda ya karanta asalin tarihin Larabawa tun a zamanin Jahiliyyah yasan ba za suzo suyi wa Annabi (saww) Kiɗan Gwauro ba don kawai matarsa ta rasu , domin ma ai ba bashi da aure bane kwata-kwata matarsa ce ta rasu ballantana ace za suyi masa kiɗan Gwauro bashi da mata ! Lallai wannan ƙissar tana kama da barkwanci sosai .
6. Da ace wannan maganar tana da asali a Tarihi da ta cike littattafan tarihin Musulunci ko shakka babu , da kuma an samu irin wannan da'awar a sauran sassa na Duniya da suke yin tashe kamar al'amarin cika ciki , sai dai bamuji sauran ƙasashe suna faɗar hakan ba ba sai a Najeriya kawai , lallai akwai alamar tambaya babba anan .
7 . Idan a Najeriya ana fara wasan tashe ranar wafatin Sayyida Khadija (a.s) goma ga wata , to ai a wata kasar 15 ga wata ake farashi ko ɗaya ga wata ko a kwanaki mabanbanta , wasu ma tsawon watan suke yi suna yi , su kuma sai muce murnar me suke yi a kwanakin da suka fara ?
Indai aka samu banbancin kwanan watan fara tashe a tsakanin ƙasashen Duniya to kenan hakan yana tabbatar mana da cewa ba wafatin Sayyida Khadija bane tushen fara tashe .
8. A hankalce kuma za mu ga lallai tashe yafi alaƙa da yanayin watan Ramadan fiye da batun Wafatin Sayyida Khadija (a.s) , domin kuwa tushen tashe a duk ƙasashen Musulmi shine murna da farinci , ko a cikin tashen ana yin waƙoƙin Azumi ne da faɗakarwa , kuma shi watan Azumi wata ne na farin ciki da faɗakarwa , kenan tashe yafi dacewa da yanayin watan Ramadan .
9. Duk wani abu da suke ƙoƙarin kafa Hujja dashi zato ne mu kuma yaƙini (sakankancewa) garemu akan Hadafin tashe , kuma a ƙa'idar Ilmi da hankali ba'a gabatar da zato (الظن) akan sakankancewa (اليقين).
10. Idan da za'a samu saɓanin ƙissoshin da suke nuna asalin manufar dalilin fara tashe , za mu iya riƙo da gaɓar da muke da tabbacin kowa ya yarda da ita a kowacce ƙasa sun haɗu akanta (wato farin ciki da murna da raha ) , sai muyi riƙo da ƙa'idar nan da Malamai suke cewa ; (التمسك بالقدر المتيقن) wato riƙo da gwargwadon da ake da yaƙini akansa , wanda wannan gwagwadon anan shine murnar Azumi , nishaɗi , raha da faɗakarwa , ba wai wafatin Sayyida Khadija ba .
11 . Idan kuma sukace duk basu yarda da waɗannan gaɓoɓi goma ba sai muce musu , kuma bamu yarda da da'awarku ba saboda shigar zai yu ba zai yu ba (الإحتمالات) cikinta , su kuma Malamai suna cewa : Idan batun yiwuwa ya shiga cikin dalilin da ake so a tabbatar da wani abu dashi to kafa hujja dashi ya ɓaci (إذا ورد الإحتمال بطل الإستدلال) , don haka ba za su iya kafa hujja da dalilinsu ba .
12. Dalilinsu ƙwaya ɗaya ko biyu ba zai iya tunkarar gomomin dalilan da suke kishiyantarsa ba , kamar gaɓoɓi goma sha ɗayan da na kawosu yanzu , kuma indai dalili yayi karo da dalilan da suka fishi ƙarfi ajiyeshi ake a ɗauki masu ƙarfi bisa ƙa'ida ta ilmi , ballantana ace zato yaci karo da yaƙini (sakankancewa) .
HUKUNCIN TASHE A SHARI'A
Dangane da mas'alar halascin yin tashe ko rashin yinsa itama abunda ake yi ne a cikin tashen ne zai yanke hukunci , me kyau ne ko mara kyau ? An shigar da abinda ya saɓawa Shari'a ciki kamar shigar mata , cutar da mutane , cakuɗuwar maza da mata da raye-raye, ki ba'a shigar ba amma ba wai tashin farko za'ayi masa hukunci gaba ɗaya ba , domin babu wani Nassi akan hakan .
Don haka alaƙar tashe da yin murnar wafatin Sayyida Khadija (a.s) maganar gaskiya bata da wani tushe mai inganci , ko tabbatacciyar madogarar tarihi ko ilmi , ta dai fi kama da shaci faɗi ko ƙiyasi da haɗa al'amura mabanbanta ba tare da dogara da wani dalili mai kyau ba , in kuma akwai karɓaɓbun dalilai ina fatan masu yaɗa wannan da'awar za su taimaka su fito mana dashi , don mu gudu tare mu tsira tare .
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏
✍️Abu HaidarAl-Abdul Faneey Al-kanaweey
https://t.me/tafarkintsiratv
12 /Ramadan/1444H - 3/4/2023 Miladiyya.