SHEKARAR BAƘIN CIKI

 



Yau 10 ga watan Ramadan , ranar tunawa da wafatin uwar Muminai Sayyida Khadija bintu Khuwaylid (a.s.) , ta rasu a shekara ta 3 kafin Hijirar Annabi (Saww) daga Makkatul Mukarramah zuwa Madinatul munawwarah.


Sayyida Khadija itace farkon wacce ta fara sadaukarwa a cikin wannan Addini na mu ta sadaukar da dukiyarta , mutuncinta , jininta da ranta don kare Annabi da tabbatar Musulunci ,shi yasa a ruwaya Annabi (Saww) yace : Ba don dukiyarta ba da musulunci bai kafu ba .


Ya ishi Sayyida Khadija matsayi da alfahari kasancewarta mahaifiyar Nana Faɗima kakar Ai'mmatu Ahlil baiti (a.s) , kuma farkon wacce ta fara miƙa wuya a cikin wannan Addini na Musulunci daga Mata , Allah ka biya mana buƙatun mu saboda Nana Khadija (a.s) da ƴaƴan ɗakinta.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post