Sharrin Media Ga Harkar Islamiyya..!!




Suna cewa Bangarorin Gwamnati Ukku ne. Amma a Hakika guda Hudu ne. Media ce ta Hudun. Kuma ta fi sauran karfi da Iko, saboda itace ke rike da Zukatan 'Yan Kasa. Ta hanyarta ne ake iya motsasu a Juyasu ko a Ingizasu su aikata wani abu, ko a kangesu daga wani Haqqi nasu, ko a cusa masu wani Ra'ayi.


Media itace Takobi mafi Hadari da Hukuma ke amfani da shi wajen Bata sunan wanda bata so. Ko daga sunan wanda yake Shafaffe da mai.


Ban San wasu gungun Jama'ah a wannan Al-umma da suka Dandani Azabar media, suke shan bone a Hannunta kamar 'Yan Harka Islamiyyah ba. Musamman Jagora Sayyid Al-zakzaky.


Media ce keda fiye da kaso 70 cikin 100 na yakarmu da bata mana suna. Fiye da Bindiga.

Musamman Shegiyar BBC nan da VOA da DHL da sauran tarkacensu na tsiya. Yanzu duk Tallafin Jagora ke rabamu Al-umma basu ga ya isa su Yada ba, saboda Alkhairi ne. Amma ana dirar mana zza kaji shegu na cewa wai an yi Arangama, ko An yi fito na fito. 'Yan Arangamar Uwa...! 


Haka suka yiwa Malam Sarki wajen Muqabala. Tun kafin taron Maja taron tsiya su ce sun Kasa shi, tuni BBC suka yada ya sha kaye. Ta hanyar kanun Labari guda, shine cewarsu: An kafama Abduljabbar Hujja da Littafin Babanshi. Kaji minafukai fah. Kaga da haka sai a rudi Bami, ace ai hatta Babanshi bai yadda da abunda yake ba. 


Hanya Daya ce ta rage mana shine mu yakesu da irin Makamin suke yakarmu dashi. Shine Media. Duk da na San ana yi, amma dole mu kara kaimi, mu canza salo. Mu fito musu ta inda basu zata ba. Da haka mu'awiya ya dinga yakar Imam Ali, da Zuriyar Gidan Manzon, ta hanyar Yada Farfaganda da Karya.


Tun Waki'ar Zariya har zuwa yau babu abunda ke cutar damu kamar media. Mu tashi mu yaketa kafin su kara mana Illa. A manta da kananan Maganganu a tunkari Manyan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post