MU'AWIYYA NE YA KASHE UMMUL MU'UMININA AISHA




A  ranar  17 ga Watan Ramadan na Shekara ta 58 bayan hijira, Mu'awiyya dan Abi Sufyan ya keta alfarmar Manzon Allah (S)!, ya keta alfarmar watan Ramadan! ya kashe ummul muminin uwar Muminai Aisha 'Yar Abibakar Matar Manzon Allah (S)!


Mu'awiyya ya yi wa ummul Muminin Aisha kisa na rashin imani da tausayi ne! domin kuwa ya haqa rami ne a fadarsa ya tura aka kira ta ta zo, da sunan zai yi sulhu da ita kan laifuffukan da take zargin sa da aikatawa, na kashe 'Yanuwanta guda biyu, da kuma dankara Dansa Yazidu mashayi a kan wuyan Al'ummar Manzon Allah (S) a bayan sa.  Bayan ya riga ya saka masu da makamai masu guba a cikin ramin! ya kuma shimfida Dadduma a kan ramin, ta yanda da mutum ya zauna zai rufta a cikin ramin ne!. 


Hakan kuwa ta faru, tana taka Daddumar sai ta rufta a ciki! masu da Qusoshi, da kibiyoyi masu guba da ke cikin ramin suka sossoke ta! Allah ya karbi ranta a cikin ramin! Mu'awiyya ya sa aka cike ramin ya zama kabarinta! hakan ta sa har yanzu ba wanda zai iya nuna maka inda kabarinta yake a cikin duniyar nan! inna lillahi wa inna ilaihi raji'uu!


Rashin son fadin labarin ne ma ta sa wasu malaman tarikhi suka nuna cewa wai ita ce ta yi wasiyya da a binne ta cikin dare, wai kamar yanda aka binne wai babanta!


DALILAN DA SUKA  SA MU'AWIYYA YA ZABI KASHE UWAR MUMINAI NANA AISHA:


1. Mu'awiyya ya tura Sojojinsa suka kashe dan uwanta Muhammad bn Abibakar, a lokacin yana matsayin gwamnan Misra ta bangaren Imamu Ali (as). Sojojin na mu'awiyya sun rutsa da shi ne suka kama shi suka sa Shi a cikin cikin mushen Jaki suka qona shi tare da mushen jakin har sai da Muhammad (R.A) ya qone kurmur kamar gawayi! inna lillahi wa inna ilaihi raji'uun! 


Hakan ta sa Aisha ta nuna bakin cikinta! da damuwarta! na kashe mata dan uwanta ba tare da wani hakki ba, har ya zama ko magana take idan ta cije sai ta tsine wa mu'awiyya a kan ta'addancin da yayi na kashe mata dan uwanta Muhammad.


2. Mu'awiyya ya nada Dansa Yazidu mashayin giya mai wasa da karnuka da birori, a matsayin magajinsa a bayansa, kuma ya sa ana bin mutane gari-gari ana karba wa Yazidun mubayi'ar zama magajinsa a bayansa!. Hakan ta sa ummul mu'uminin Aisha da ma Sahabban Manzon Allah (S) da yawan gaske da ke Madina, suka bayyanar da kin yardarsu da bijirewarsu, da tawayensu, a sarari kan wannan yunkuri na mu'awiyya na nada dansa mashayin jiya (Yazidu) a matsayin shugaban Al'ummar Manzon Allah (S), daga ciki kuwa har da Abdurrahman, Shi ma dan uwan Aisha din ne, kuma Shi ma Mu'awiyya ya sa an binne shi ne da ransa har lahira! kamar yanda Ibnu Kathir ya hikaito a cikin AL-BIDAYA WAN-NIHAYA juzu'i na 8 shafi na 123.


Hakan ta sa Mu'awiyya ya ji tsoron kada ta sa a yi masa bore kan wannan danyen aiki da ya aikata ga 'yan uwanta guda biyu MUHAMMAD, da ABDURRAHMAN, kai tsaye ya ga cewa kashe ta ne kawai mafita a gare shi, domin ya tabbatar da cewa idan ta hawo Rakumi ko Alfadari da shirin yakar sa, lallai da yawan mutane za su goya ma ta baya ne.


Wadan can dalilan suka sa mu'awiyya ya yanke shawarar kashe ummul muminin Aisha, domin gudun kada ta kawo masa matsala kan yunkurin sa na karba wa Yazidu bai'ar zama khalifa a bayan shi, musamman ma a garin Madina.


Ina masu yawo da karairayi da sharrace sharracen cewa wai shi'a na zagin matan manzan Allah (S)! wa iyazu billah! to mu kam ba wata daga cikin matan annabi da muka taba zagi, ko muka taba yi wa karya ko sharri.  Amma idan kuna neman makiyan Matan Manzon Allah (S) ne, to ga Mu'awiyya nan, Shi ba ma maganar zagi ba, a'a kashe Matar Ma'aiki (S) ya yi! kuma kisa na rashin imani da tausayi!


Ya Allah ka Shaida cewa: Mun barranta, mun yi Allah wadai, mun yi tir! da wannan kisan da Mu'awiyya yayi ga Uwarmu Aisha 'yar Abubakar, ba laifin tsaye ba na zaune, kawai domin ya kashe mata 'yan uwanta guda biyu, ta nuna rashin amincewar ta!. Kawai domin ta ki yarda da nada Yazidu dan giya mai wasa da birai da Aladu! a matsayin Khalifa mai jiran gado.


Ya Allah ka bi mana hakkinmu a kan wannan ta'addanci da Mu'awiyya yayi ga Matar Annabinmu, a cikin Wata mai alfarma na Ramadan. Kuma ya Allah ka tsine wa masu Kashe matan Annabi (S).


Mai neman yin bincike kan abin da aka rubuta sai ya je ya duba littafin : 


1. Dabaqaatul kubra na Muhammad bn Sa'ad  juzu'i na 8 shafi na 77. 


Da kuma:


2.  Al bidaya wan-nihaya na Ibnu Kathir juzu'i na 8 shafi na123.


Da kuma:


3. Tahzibul kamali fi asma'ir-rijali,  na Yusuf bn Abdurrahman Al-Kalbi, juzu'i na 35 shafi na 235.


Da kuma:


4. Ansabul asharaf, na Balaziri.


Da kuma:.


5. Tarikhud-dabary juzu'i na 6 shafi na 50.


Da kuma:


6. Sharhin Nahjul balaga na Ibnu abil hadid Al-mu'utazili.


    --Jawad Adamu Tsoho

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post