Wannan na daga cikin tambayoyin da dayawan Mutane suke yi , wasu kuma maƙiya Shi'a ne suke yawan kawota a matsayin Shubhar da za su yaƙi Shi'a da ita , suna masu cewa Shi'a basa son Imam Hassan ko sun fi fifita Imam Hussain akansa , tunda gashi a cikin Imamansu ma ba ƴaƴan Imam Hassan (a.s) tare da cewa ya girmi Imam Hussain (a.s) .
AMSA
Shi Imamanci zaɓin Allah ne ba zaɓin Mutane ba , Allah ne yaga dama yaso ya sanya Imamai tara a zuriyar Imam Hussain (a.s.) banda waninsa, kuma shi Allah ba'a tambayarsa akan abinda yake aikatawa na hukunci a cikin bayinsa amma su bayi ana tambayarsu abinda suke aikatawa , kamar yanda yazo a Alkur'ani ;
لَا يُسْـَٔلُ عَمَّا يَفْعَلُ وَهُمْ يُسْـَٔلُونَ .
Kamar yanda Allah yaga dama ya sanya cikamakin Annabawa Manzon Allah (saww) a zuriyar Annabi Isma'il bai sanya shi a zuriyar Annabi Ishaq (a.s) ba , tare da cewa dukkansu ƴan uwa ne kuma Annabawa ne , bari ma da yawan Annabawa sun fito daga tsatson Annabi Ishaq ne amma banda Annabi (saww) .
Haka nan Annabta a zuriyar Annabi Ya'aƙub (a.s) ta kasance ga ɗaya daga cikin ƴaƴansa sha biyu ba duka ba .
Haka nan Allah bai sanya Annabta cikin zuriyar Annabi Musa ba sai ya sanyata a zuriyar Annabi Haruna (a.s) .
Shi ɗan Annabi Nuhu da Allah ya bada Labarinsa cikin Alƙur'ani ma bai kasance daga cikin masu tsira ba ya kasance cikin halakakku ne , ba ma ana maganar zamansa Annabi bane a'a , ya kasace cikin halakakku ne sai Annabta ta zama a sashin ƴaƴan Annabi Nuhu (a.s) ba dukkansu ba .
Shin wannan bai nuna cewa Allah Ta’ala ba yana zaɓar Annabawa da magadansu a kan asasin nasaba da kusanci ba ? Kaɗai hakan yana kasancewa bisa ga wasu ma’aunai da dalilai, waɗanda nasabar za ta iya yin wani tasiri, ta yadda take zama lamari mai taimakawa wajen nuna tsarkinsa da girmansa da ɗabi'unsa, domin Allah baya sanya Annabawa da Wasiyyai a cikin mutanen da ba ƴan manyan gida ba .
Anan ba za mu ce me yasa Allah yayi hakan ba ? saboda ya riga ya bamu amsa a cikin Alkur'ani inda yake cewa:
اللهُ أَعْلَمُ حَيْثُ يَجْعَلُ رِسَالَتَهُ ۗ
Allah shi kaɗai yasan inda yake ajiye saƙonsa kamar Annabta da Manzanci da Imamanci , indai yayi hukunci ba abinda ya ragewa bayi in banda sallamawa da miƙa wuya , domin shine mafi sanin maslaharsu da abinda yake alkhairi garesu.
Jahilai ne da maƙiya Shi'a suke yaɗa ai wai Shi'a basa son Imam Hassan (a.s) Astagfirullah ! Sun manta da abun Zaɓin Allah ne ba na mutane ba balle su zaɓi wanda suke so .
Kuma mu yan Shi'a a wajenmu Imam Hassan yafi Imam Hussain (a.s) daraja da matsayi a wajen Allah Ta'ala, don haka ba wai zaɓin mutane bane abun sam , Allah ne yake yin yanda yaso da lamarinsa bisa hikima da maslaha da adalci .
Ai ba Imam Hassan ba akwai ya'yan Imam Ali (a.s) dama shi Imam Hussain (a.s) ɗin da yawa da basu zama Imamai ba , sai ace don me yasa ? A'a , idan da Shi'a basa son Imam Hassan kamar yanda jahilai ke riyawa ai da shima ba za'a ga sun saka shi a cikin jerin Limaman shiriya ba gaba ɗaya .
Girmewa a shekaru ko ƙarantarsu bashi da alaƙa da Imamanci sam , domin a cikin Imamai akwai wanda babban ɗansa ya zama shine Imami a bayansa (kamar Imam Ali da Imam Hasan a.s) , akwai kuma wanda ba babban bane ya zama hakan (kamar Imam Ja'afar Assadiq da ɗansa Imam Musal Kazim a.s) .
A taƙaice dai wannan Shubha da ba ta da ma'aunin ilmi da hankali salimi .
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
Sha'aban/1444H - 12/3/2023 C.E.