LOKACIN BUƊE BAKI ! ME YAYI ZAFI HAR MUKE WUCE GONA DA IRI DA KAI RUWA RANA AKAI ???

 


1. Mafi yawan Malaman Shi'a Imamiyya (Musamman ƴan baya da ƴan zamninmu ) sun tafi akan lokacin Sallar Magriba ko buɗe baki shine bayan faɗuwar rana da shigar dare ( lokacin da jan gabas ya ɗaukewa kenan ) , wasu sunyi fatawa ne akan haka , wasunsu kuma ihtiyaɗi ne na wajibi jiran shigar daren kamar fatawar Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Sistani (H) da Malaminsa Ayatullahi Sayyid Khu'i (Rahimahullah) ,  kuma sun dogara da wasu Ayoyi da Hadisai ne ba wai shaci faɗi sukayi ba .


2 . Wasu kuma a Malaman Shi'ar sun ce : Ba buƙatar sai dare ya shiga da zarar rana ta faɗi lokacin buɗe baki ko sallar magariba yayi kamar yanda dai Ahlussunah waljama'a suke yi , Waɗannan malaman na Shi'a suna ganin ɗaukewar wannan jan na gabas dan samun nustuwa da tabbaci ne kawai amma ba dole bane , ana kuma danganta wannan ra'ayin ga wasu manyan magabatan Malaman na Shi'a , Kamar Assaduƙ , Aɗɗusi a sashin wasu ra'ayoyinsa , Almurtadha ,  kuma har a ƴan zamaninmu akwai masu wannan ra'ayin , kamar Ayatullahi Sayyid Muhammad Sa'idul Hakeem , Ayatullahi Fadlullahi , Ayatullahi Sayyid Muhammad Rohani , Ayatullahi Bahjati , Ayatullahi Sabzawari da sauransu , sannan suma bawai molan ka sukeyi ba , suna da dalilan su daga ruwayoyi domin akwai kusan ruwaya Ashirin (20) ko fin haka ma da suke nuni da shan ruwa da zarar rana ta faɗi , kuma mafi yawansu ingantattu ne ba batun rauni a isnadinsu , batun ayar shigar dare kuwa suna bata mafita da tafsirin Luga , urfi da suna'a Fiqhiyya , abun dai ba na gama gari bane Irina da irinka .

Uwa uba Riwayoyin Shi'a da suke bayyana lokacin buɗa baki shine faɗuwar Rana ba ɓacewar jan Gabas ba su suka fi yawa da ƙarfin Isnadi .


3 . Su kuma Ahlussunah waljama'a suna ganin indai rana ta faɗi to fa lokacin shan ruwa yayi , ba buƙatar wani ɗaukewar jan gabas ko shigar dare kamar dai ɓangare na biyu a gidan Shi'a , tare da cewa a cikin litattafansu akwai ruwayoyin da suke nuna wajabcin shigar dare kafin buɗa baki amma dai saɓanin haka Malamansu suka yi ijma'in fatawa da aiki .


GYARA KAYANKA 


Don haka , batun gaskiya dangane da  yadda ya kamata mu ɗauki wannan mas'alar shine : 


A. In Kai ɗan Shi'a ne ka koma wajen Mujtahidin da kake taƙalidi dashi kaji fatawarsa akan haka , sawa'un cewa yayi : Ka jira jan gabas ya ɓace ko cewa yayi da rana ta faɗi ka sha ruwa , ba buƙatar sai ka soki wani ta ƙarfi da yaji , bayan kuma ƙofar tattauanawar ilmi da dalili a buɗe take , to me yayi zafi har ta kai ga rigima da kai hari a cikin mas'alar saɓani irin wannan da har a gidan Shi'ar akwai sabani !


B . idan kai Ahlussunah waljama'ah ne kaje kasha ruwanka da zarar Rana ta faɗi , ba buƙatar sai ka soki ɗan Shi'a ko kace sai yayi irin naka , amma dai ka sani ɗan Shi'a zai iya kafa maka hujja da littattafanka akan lokacin buɗe baki shine zuwan dare ba faɗuwar rana ba , ya zo a mafiya ingancin littattafan Ahlussunna Wal jama'a Annabi (saww) ya ce : Sai rana ta faɗi dare ya gabato ake buɗa baki . Ya zo a Muwaɗdar Maliku cewa : Umar bn Khaɗɗab da Usman bn Affan basa shan ruwa sai sunyi sallar Magriba dare ya shiga a watan Ramadan . 

Ya zo a Tafsirin Ɗabari cewa : Umar Bin Khaɗɗab yayi bayanin lokacin buɗe baki shine shigar dare , da wasu dalilan na nan jingim a bangaren Sunni .


A ganina mas'alar bata buƙatar kai ruwa rana kamar yanda dayawan mu suka ɗauketa , Ni yanzu lokacin shan ruwa a wurina shine shigar dare ba faɗuwar rana ba , kuma ko gezau bazan ba dan naga ɗan Shi'a yasha ruwa irin na Ahlussunah waljama'a  don ban san dawa yake Taƙalidi ba , hakanan bazan sawa kaina tashin hankali ba dan naga ɗan Ahlussunah ya sha ruwa da zarar faɗuwar rana , domin nasan Fiƙhunsa ne ya koya masa haka , wani karin maganar Mutanen Iraƙi yana cewa : kowa da shari'arsa , Musa da shari'arsa Isa ma da Shari'arsa , wani mawaƙi kuma yana cewa : ka tsaya a inda kake na taya a inda nake , Karka soki inda nake , kar na soki inda kake .... Allah Ta'ala kuma ya ce : لكم دينكم ولي دين


Allah yasa mu dace , ya kuma karbi ibadun mu , Amin .


✍️ Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 


3/Ramadan/1443H - 25/3/2023 Miladiyya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post