Ba kasafai Shehu Nasiru Kabara (Rahimahullah) ya cika ambatar sunan Manzon Allah (Muhammadu) ba a cikin Diwaninsa da Talifofinsa , yakan sakayya sunan Annabi (saww) a mafi yawan Ƙasidunsa saboda tsananin girmamawa ga Manzon Allah (saww) sai dai ya ambaceshi da sauran Siffofinsa da Laƙubansa na ban girma kamar : Annabi , Shugaba, Rasulullah, Ɗaha , Khairul Warah da sauran sunayen Annabi (saww) masu Girma .
Kuma wannan tamkar Karantarwa ce ta Alƙur'ani mai girma , domin kuwa a wurare Huɗu kacal Allah ya ambaci sunan Annabi ƙarara da "Muhammadu" a ko da yaushe yakan kirashi da Nabiyu , Rasulu , Ra'ufu , Rahimu ko ma da lamirin suna don girmamawa gareshi .
Babu shakka tsananin soyayya da ban girma ke sa masoyi ya dinga jin nauyin ambaton sunan masoyinsa ƙarara ba tare da ya sakayashi ba .
Wani abun sha'awa wannan ban girma da Sheikh Nasir Kabara yake yiwa Annabi (saww) ta hanyar sakaya sunansa "Muhammadu" tun a Duniya ya fara samun sakamakon hakan kafin lahira , ta yanda ya zama a al'adar mafi yawan Mutanen garin Kano in suka haifi yaro suka sa masa sunan Shehin (Nasir) basa ambatan Yaron da sunan ɓaro-ɓaro sukan sakayashi da wasu Laƙubba kamar : Mai Kabara , Mai Sunan Malam , Na Kabara , Al-maliki duk don Girmamawa ga Shehun , Musamman ma Ƙadirawa .
Dama Hausawa sunce "Duk abinda kayi za'a a yi maka shi , kuma duk abinda ka shuka shi za ka girba na Alkhairi ko Sharri .
Tabbas Sheik Nasir Kabara ya shuka soyayyar Manzon Allah (sawa) da girmama shi kuma yanzu ba ma shi ba har jikokinsa suna cin gajiyar wannan alkhairin da ya shuka a zuƙatan Masoya Annabi (saww) .
Alhamdulillahi , mun sha daga wannan Babbar Halara da suka shayar damu daga ita cikin soyayyar Annabi (saww) da girmama sunansa .
Shehu Busiri cikin Alburda yana faɗa cikin Haƙƙin sunan Manzon Allah da girmansa :
لو ناسبتْ قدرهُ آياتهُ عظمًا
أحيا اسمهُ حينَ يُدعى دارسَ الرِّممِ
لَمْ يَمْتَحِنَّا بما تعيى العُقولُ بِهِ
حِرْصًا علينا فلمْ نرتب ولَمْ نَهَمِ
Allah ya jadadda rahama da gafara ga Sheik Muhammad Nasiru Kabara , yayi albarka ga zuriyarsa da masoyansa baki ɗaya .
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
Sha'aban/1444H - 15 /3/2023 C.E.