Sunanta Habbatu ƴar Ja'afar (Rahimahallah) , nasabarsata tana komawa ga Walibatu daga Bani Asad shi yasa ta shahara da suna Walibiyyatul Asadiyya , ana yi mata Alkunya da Ummunadah, kamar yadda ta shahara da sunan ma'abociyar dutse , saboda mu'ujizar da ta faru da ita a hannun Imaman shiriya (a.s) da ta tabbatar da gaskiyar Imamancinsu a bayan Manzon Allah (saww) , ta yanda ya zama Imam Ali (a.s) yayiwa wani dutse da ya bata Stamfi da zobensa kuma wannan sitamfi ya wanzu a jiki , kamar yanda irin wannan mu'ujizar ta faru da wasu mata biyu da ake musu Alkunya da Ummu Ghanim da Ummu Saalim, kuma duk su ukun sun shahara da sunan ma'abota dutse (tsakuwa) .
ASALIN ƘISSAR MU'UJIZAR DA TA FARU DA ITA A ZAMANIN AI'MMATU AHLIL BAITI (A.S) .
Sheik Alkulaini ya ruwaito a cikin Alkafi cewa : Habbabatul Walibiyya ta nemi Imam Ali (a.s) ya bata wani dalili da za ta riƙeshi a matsayin gaskiyar Imamancinsu , take Imam yayi mata ishara ta ɗakko masa wani dutse , yayin da ta miƙo masa dutsen sai buga wani Sitamfi a jikinsa da zobensa kuma yace da ita " Duk sanda wani yayi da'awar Imamanci kuma kika bashi dutsen nan yayi irin Sitamfin da nayi to kisani shi imami ne da ya wajaba ayi masa biyayya ".
Bayan shahadar Imam Ali (a.s) sai Habbabatu ta kawowa Imam Hasan (a.s) wannan dusten kuma ya buga masa sitamfi kamar yanda mahaifinsa Imam Ali (a.s) yayi , haka a bayan Imam Hassan Imam Hussain (a.s) yayi mata , haka tai ta bawa duk Imamin da ta haɗu dashi yana yiwa wannan dutse sitamfi har lokacin Imam Ali Arridha (a.s) shima yayi mata sitamfin a jiki .
Shehunmu Assaduuq da Aɗdabrasiy ma duk sun ruwaito wannan Riwayar.
WASU KARAMOMIN DA SUKA FARU DA ITA A HANNUN AI'MMATU AHLIL BAITI (A.S) .
An ruwaito daga cikin karamomin da suka faru da ita a cikin babin da ya shafi Imamanci da karamar Ai'mma (a.s) :
1. Allah ya yaye mata cutar kuturta a hannun Imam Hussain (a.s) ta samu waraka kamar barayi ba .
2. Sake maida ita budurwa da Allah yayi a hannun Aliyu Zainul Abidiin (a.s) bayan ta tsufa tukuf, lokacin tana da shekaru 113 cif .
3. Lokacin da furfura ta cinye gashinta yayi fari fat , Allah ya maida mata shi baƙi siɗik da albarkar Imam Muhmmadul Baƙir (a.s) .
4. Allah yayi mata tsawon rai albarkacinsu ta yanda ta rayu sama da shekara 230 , dama wasu mu'ujizozin da aka ambata a babin karama da gaskiyar Imamatu Ahlil baiti (a.s) .
WAFATINTA
Habbabatu tayi tsawon rai har lokacin Imam Ali Arridha (a.s) , bayan ya gamu da Imam Ridha (a.s) da wata tara ta koma ga Allah , a lokacin yayi mata Ninkafani da rigarsa mai albarka ya kuma yi mata Sallah , ko a lokacin da taso zai mata addu'a ta cigaba da rayuwa ko shakara nawa take so .
An ambata cewa ta rayu a Duniya tsawon shekaru Ɗari biyu da Talatin (230) , kuma wannan ba komai bane daga cikin ikon Allahn da yasa Annabi Nuhu ya kashe shekaru 950 yana da'awa .
Habbabatul Walibiyya - kamar yanda Malaman Hadisi suka ambata - ta kasance maruwaiciyar Hadisai kuma ta Rawaici Hadisai daga Imam Hassan , Imam Hussain, Imam Sajjad da Imam Muhammadul Baqir, wasu suka ce har daga Imam Ali (a.s) ta Ruwaici Hadisi , Shehunmu Assaduuq ya kawo Ruwayoyinta a cikin Littafinsa (من لا يحضره الفقيه) .
Allah ka biya mana buƙatunmu sabida karama da isar Ahlul baiti (a.s) .
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
https://t.me/tafarkintsiratv
15/ Ramadhan/1444H - 6 /3/2023H .