KASANI:- Neman Taimakon Mazon Allah (s) Shi ne Hakikanin Neman Taimako A Wajen Allah (t). _ Abu Haidar Al-Abdul Faneey Al-kanaweey

 


Isa da darajar Shugaba (saww) a wajen Allah tasa ake fakewa dashi don a samu yarda da taimakon Allah , taimakon nan da ake nema a wajensa shine ainihin taimakon da ake nema a wajen Allah , domin duk abinda Annabi (saww) yake bayarwa na Madadi da kwaranye to kai tsaye daga Allah yake , don haka babu banbanci da abinda shugaba yake bayarwa da wanda Allah yake bayarwa ɗan juma ne da ɗan Juma'a , jahilai da jakuna ke raba ɗaua biyu .


Misali , masu fakewa da wani Hadimi ko makusancin Shugaban ƙasa don samun wata biyan buƙata a cikin Gwamnati, suna zuwa wajen wannan makusancin na shugaban ƙasa don ya zame musu tsani zuwa ga cimma muradinsu za amma shi kanshi yasan ba'a wajensa suke nema ba , kuma ko sun nema a wajensa basu tafi wajen shugaban ƙasa kai tsaye shi kanshi yasan duk abinda zai basu daga arzikin shugaban Ƙasan ne , a wajensa ya samu ko me zai bawa wani .

To shima kusan haka manzon Allah (saww) , duk wani abu da zai bayar daga Allah yake , bayarwarsa bayarwar Allah ce Mahjubai ne suke raba ɗaya biyu .

Wai ma menene matsala ko mutum ya ƙudirce Annabi ne yayi masa wannan ba kowa ba ? Inda matsalar take yaji cewa Annabin akan kansa yayi masa ba daga Allah ba , ko idan ya kore mashi'a da tasirin Allah .


Ma'ana Allah ya riga ya bawa Annabi (saww) komai yayi yanda ya ga dama dashi da izininsa .

Don haka tsantsar Jahilci da zindiƙanci ne mutum yace wai shirka nc neman taimako a wajen Manzon Allah (saww) .... Astagfirullah.


In har yin hakan shirka ne to shine babban mushriki mai maganar , domin kullum yana neman taimako sau ba adadi a wajen wanin Allah ;


In yaji yunwa yana neman taimakon abinci dan ya magance masa matsalarsa ta yunwa , idan yaji ƙishirwa yana neman taimakon ruwa dan ya magance masa ƙishirwa, me yasa bai ɗaga hannu ya roƙi Allah kai tsaye ya dauke masa mstalarsa sai ya koma ga wasu bayin Allah , domin yunwa da ƙishirwa ai suma bayin Allah ne , kenan ya zama Mushriki ?! 

Haka yana neman taimakon ƴam uwansa mutane dan su yaɗa masa karatukansa dan ya samu ladan da zai kusantashi da Allah , kenan shima yayi tawassuli da kamun ƙafa da wanin Allah Ta'ala ciki har da wawayen da suke ihu da kabbara a gabansa da ƙattan da suke yaɗa masa karatunsa ? 


Sunce ba'a kamun ƙafa da Annabi (saww) dan neman kusanci ga Allah amma kuma za ka iya yin aiki na gari - ko da sharar kwata ne - ka nemi kusanci ga Allah dashi , to shi wannan aikin alkhairin ba wanin Allah bane ko ba bawan Allah bane ? Ina suka bar : 


وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ


Tarin dalilai na hankali da Ayoyin Alkur'ani da Hadisai masu yawa da inganci sun tabbatar da Halascin neman taimako a wajen wanin Allah , tare da yin kamun ƙafa dashi dan samun kusanci ga Allah , matuƙar dai mutum bai ƙudirce "Istiqlalalin" ikonsu ba tare da Kore mashi'a da ikon Allah , amma Indai ka ƙudurce cewa duk abinda nake nema a wajen wannan bawan Allah zai yi min ne da izinin Allah to wannan shine tsantsar Tauhidi , domin ka ɗayanta duk wani tasiri da iko ka maida shi zuwa ga Allah , ina nufin :

 لا مؤثر في الوجود إلا الله .


Wannan itace sunnar da Musulmi suke kanta tun zamanin Annabi da Sahabbansa da Tabi'ai da waɗanda suka biyo bayansu da aiki na gari duk sun Kasance suna neman Taimakon Annabi , suna yin Tawassuli da Istigasa dashi , har sai da wata babbar Annoba da ake kira Ibnu Taimiyya ta bayyana a ƙarni na bakwai , sannan ya fara sukar batun tawassuli da Istigasa , bayansa kuma su Muhammad ɗan Abdulwahhab suka sake raya Makarantarsa tare da tufafin Wahhbiya , Salafiyya , Izala da Boko Haram har ta kai ga an sami irinsu Dakta Jaki Suna taɓa janabin Annabi da sunan Ilmi da Malanta , duk da an cuci Jaki da aka haɗa shi dashi a suna .

 

وَلَقَدْ ذَرَأْنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيرًا مِّنَ الْجِنِّ وَالْإِنسِ ۖ لَهُمْ قُلُوبٌ لَّا يَفْقَهُونَ بِهَا وَلَهُمْ أَعْيُنٌ لَّا يُبْصِرُونَ بِهَا وَلَهُمْ آذَانٌ لَّا يَسْمَعُونَ بِهَا ۚ أُولَٰئِكَ كَالْأَنْعَامِ بَلْ هُمْ أَضَلُّ ۚ أُولَٰئِكَ هُمُ الْغَافِلُونَ (الأعراف/ 179)  .


Zan cigaba Insha Allah ......


Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏


✍️ Abu Haidar Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 


14/Ramadan / 1444H - 4/4/2023 Miladiyya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post