JAHILCI IN YA GWAMU DA KISHIN ADDINI.....

 


Marhum Sheikh Muzaffar ya kawo a littafin sa na Mandiq cewa, Jahilci iri biyu ne.


Akwai Jahil Murakkab da Jahil Basid.


Shi Jahil Murakkab; Shine Jahilin da bai fahimci cewa shi Jahili bane, yana daukar kansa cewa ya sani, alhali kuma bai sani ba, sai Jahil Basid, shine Jahilin da ya fahimci Jahilcinsa, shi bai sani ba, amma ya yarda da cewa bai sanin ba.


Shi Jahil Basid, ana iya kamanta daliban ilmi da shi, wadda suke naiman sanin abinda basu sani ba, kuma kowa zai iya zama Jahil basid akan abinda yake da bukatar sani da bai san shi ba.


Yanzu ni Jahil basid ne a bangarori da dama, kamar aikin likitanci, Injiniya ko Kwamfuta da sauran su, kuma na fahimci Jahilci na, harma ina son naga na fita daga kangin wannan Jahilcin.


Babban abinda ke damun duniyar Musulmi a wannan yanayin, hatta wadda muke musu kallon Maluma, su Jahilai ne a bangarori da dama na Addini, amma sun tsinci kansu a layin Jahil murakkab, basu sani ba, basu kuma yarda akan basu sani ba, akan rashin sanin nasu da tsinannan taurin kai, suna ta halakar da bayin Allahn da suma basu sani ba.


Shiyasa in Jahilci ya gamu da kishin Addini a kwakwalwar mutum, yakan rikide yafi dabbar daji illa a cikin mutane.


Ga wani misali, lokacin da ISIS suka ci karansu ba babbaka tsakanin Iraqi da Syria, an samu Matasa masu kishin Addini, amma kasancewar su Jahilai kuma a Ajin murakkab, sai suka dinga ta'adanci da sunan a Musulunci sukewa aiki. Na san tagwayen da suka yanka mahaifiyar su akan ta musu nasiha su bar abinda suke da sunan Addini a Saudiyya. 


A kurkusa, munga yadda Matasa suka shiga da'awar Muhammad Yusuf da ake kiran ta da Boko-Haram a hanun yan jarida, akwai wata zantawa da akai da wani da aka kama, akan meyasa kuke kai hare hare cikin kasuwa, Masallatai da Cocina, sai yace a dalilin kashe kafiri 1, sai Musulmi da yawa suka mutu, to su Musulmin zasu tafi Aljanna, shi wannan kafirin da akai aiki akansa, zai tafi wuta.


Meyasa suke da irin wannan tunanin? Saboda suna aiki da Kiyasi, kawai abinda kwakwalwar su ta basu, zasu hada da abinda suke gani a Zahiri, sai su zartar da hukumci, kuma dole ka yarda wai har a wurin Allah, wannan hukuncin haka yake.


Meyasa mutum Namiji zaiyi fitsari, kuma ta wurin da yake fitsarin tanan maniyyi yake fita masa, amma a shari'a aka ce yai tsarki da ruwa, zai kautar da fitsarin, amma sashin maniyyi wanka zaiyi? In zakai hukunci da kiyasi, to kowannen su zai dauki hukuncin daya, imma Wanka ko tsarki da ruwa ya wadatar, wadda a Addini ba a haka, komai akwai Ahl-iktisas din shi, shiyasa muke komawa ga Maraji'ai akan mas'alar Addini, abinda ya shafi rashin lafiya mu tafi Asibiti wurin likita.


Tunda na gane bambamcin Jahil Basid da Murakkab, maganar gaskiya zagi a Addini ya daina bata min rai, imma ka zage ni, kan kayi zagin an zagi dubu na, imma yabo ne haka abinda yake, saboda na san kishin Addini ya gwamu da Jahilci a kwakwalwar mutum, hatsarin wannan mutumin maganin sa saide Allah, saboda hatta mutuwa zai zabe ta, kuma a dukkan tunanin sa yana yiwa Allah abinda yake so ne.


Shiyasa Allah ta'ala yake cewa, "Kasanni kafin ka bauta min, in baka sanni taya zaka bauta mini? ".


Maluman Aqida sun kawo cewa, da yawan mutane zasu tashi ranar lahira, da tunanin duk wahalhalun da suke sha, bauta suke wa Allah, sai an je lahira mutum yaga ashe ba Allahn da ya turo Annabi Muhammad (S) yake bautawa ba, son ransa yake bautawa.


Kuma Arifai suna cewa, yayin da mutum ke sallah, in yazo wurin karanta "Iyyaka na'abudu....", to duk abinda yazo ransa a wannan gabar, shi yake bautawa.


Saboda haka ba a Addini da Jahilci Ajin murakkab, baka sani ba ka dauka ka sani, kuma ba'a Addini da yayi ko su wane da wane ma shi suke yi, ko kuma wai ka tashi kaga abinda Iyayenka suke kenan, ana Addini da Hujjah ne, saboda zamanin Hujjah (AF) muke, kuma Allah da Hujjah ake tunkararsa ba da hasashe ko ina ganin haka yakamata ba.


Allah ta'ala ya tausaya mana.


Muhd Bala Afuwa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post