-Imam Ali (AS) Yace: "Duk Wanda Ya iya Hana Kansa Wasu Abubuwa Guda Hudu, to Ya Kubuta Daga Afkawa Cikin Tsautsayi Har Abada".

 



-Sai Sahabban Imam Suka Ce Wanne Abubuwa Ne Ya Shugaban Muminai?


-Sai Imam Ya Amsa da Cewa:


 (1) Gaggawa.

(2) Taurin Kai.

(3) Girman Kai.

(4) Rashin Kula.


-Daga Littafin Tuhaful- Ukul Shafi Na 222).


-Ƙarin Haske Kan Wannan Hadisin Shine: Duk Wanda Ya Nisanta Kansa Daga Wadannan Siffofi Guda Hudu, Shi Kadai Ne Ko Kuma Wata Jama'a Ce ta Shugabanni da Jagorori, to Babu Wani Hatsari da Tsautsayi Na Bacin Rai da Zai Auku A Kansu:


1- Gaggawa, Wato Yanke Shawara Cikin Hanzari Ko Gudanar da Wani Aiki Ba Tare da La'akari da Abin da Zai je Ya Komo Ba. Amma Gaggawa A Nan Ba Tana Nufin Yin Sauri Wajen Gudanar da Aikin Alkhairi Bane. 


2 - Shi Kuma Taurin Kai Yana Ɗaya Daga Cikin Matsaloli Masu Hatsari da Bala'i Dake Addabar Al'umma. Wato Dagewa Kan Abu Ko Matsin Lamba Kan Rashin Gaskiya Kan Wani Abu da aka Furta Ko Mataki da Aka Ɗauka Kuma Mutum Ba a Shirye Yake Ya Janye Daga Kan Matakin Ba ko da Kuwa Ya Tabbatar da Rashin Ingancinsa. 


3 - Girman Kai, Wato Yaudaran Kai da Fankama da Mutum Yake yi Domin Allah Ya Lullube Tawaya da Rauninsa, Wani Lokaci ma Ya Dinga Fankama Kan Kyawawan Ayyukansa.


4 - Rashin Kula da Lalaci da Nuna Rauni Kan Muhimmin Lamari, Wanda Aikin da Ya Kamata Mutum Ya Gudanar A Yau Sai Ya Jinkirta Shi Zuwa Gobe da Haka Zai Janyo Mai da Hannun Agogo Baya.


-'Yan uwa Wannan Hadisin Na Shugaban Muminai Imam Ali (AS) Tabbas Hadisi Ne da Ya Kunshi Dukkanin Hikima, Sannan Kuma Dukkanin Cutarwa da Hasara da Al'umma Take Fama Da su Sun Samo Asali Ne Daga Wadannan Al'amura.


-Don Haka Muna Rokon Allah Yasa mu Dace da Mikewa Domin Gwagwarmaya Tare da Tallafawa Daga gare shi Wajen Kauracewa Wadannan Munanan Siffofi.


-Muna Fatan Allah Ta'ala Ya Bawa  Su Sayyid (H) da Malama Zeenatuddeen Lafiya.


-Muhammad Jiddah Nguru.

07037009525

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Allah (T) Ya saka da alheri Kuma wannan hadisi ya zama hujja gare mu ba a kan mu ba

    ReplyDelete
Previous Post Next Post