____Sani Hamisu.
Ya zo a ruwayoyi cewa, idan budurwa
ta isa aure amma ba ta samu miji ba,
to a rinka yi mata (kuma ita ma ta
rinka yin) wuridin wannan ayar :
"innallazhiyna Yatluna Kitaballahi,
Wa'akamus Salata, Wa'anfaku Mimma
Razaknahum Sirran Wa'alaniyatan,
Yarjuna Tijaratan Lan
Tabour!" (Jamalul - Usbu'i, shafi na
122).
Haka nan duk maccen da take
karantawa ko ake karanta mata
'Suratud - Dalaak' kafa 21,da nufin
Allah ya kawo mata masoyi wanda zai
aureta to za ta samu mijin aure ba da
dade wa ba insha Allah '(Mujarrabatul
Imamiyyah, 190),
Daga Littafin Taskar Alheri, na Malam
Adamun Adamawa.daga Musa ahmad