Wani dalibin ilmi ya tambayi Malaminsa kamar haka, Meyasa ake cewa a Watan Ramadan ana daure shaidanu, amma ga shi a zahiri muna ganin mutane na aikata sabon Allah?.
Sai Malamin yace tabbas yazo a ruwayoyi ana daure shaidanu, amma abinda Allah ta'ala yake so ya nuna anan shine, duk wadda yaga yana aikata wani aiki na Zunubi a irin wannan wata mai Falala, shine Shaidan din kansa, kuma hakan Izina ne ga wadda za suyi jayyah da Iblis ranar lahira, suna kiran ka cuce mu yana fadin kuka cuci kanku.
Allah ka tsare mu ga sharrin kawukanmu.
-Muhd Bala Afuwa