A ranar sha biyar ga watan Ramalana mai albarka na
shekarar hijira ta uku, gidan Annabci ya sanar da haihuwar
jikan farko, nan take sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya garzaya
zuwa gidan Fatima (a.s.) don sadar da taya murna da farin
cikinsa.
Bayan isowarsa, sai aka gabatarwa Manzo (s.a.w.a) da
abin haihuwa mai albarka, Manzo ya tarbe shi, ya dauke
shi a hannunsa, ya sumbace shi, ya rungume shi a kirjinsa;
sai kuma ya kira salla a kunnensa na dama, ya yi ikama a
na hagu da sautin gaskiya da ya zama farkon sautin da ya
fara ratsa samuwarsa da jinsa. Sai Manzo (s.a.w.a) ya
waiwayi Ali (a.s.) ya ce: “ Wane suna ka sa ma dana ? ” sai
Imam Ali (a.s.) ya ce: “Ban kasance mai shiga gabanka ba “,
sai Manzo ya ce: “ Kamar yadda ban kasance mai shiga
gaban Ubangijina ba ”. Wannan tataunawa ba ta kai
gacinta ba sai ga wahayin Allah na saukowa ga Manzo
(s.a.w.a), wanda ke sanar da shi cewa Allah Madaukaki Ya
sanyawa abin haihuwan suna Hasan .
Lokacin da kwanaki bakwai da haihuwa suka kewayo, sai
Manzo (s.a.w.a) ya sami rago ya yi masa akika (yankan
suna) da shi, daga ciki ya ba unguwar–zoman da ta karbi
haihuwarsa cinya tare da dinari guda, wannan a matsayin
godiya bisa kokarinta a madadin abin haihuwa da
mahaifiyarsa mai tsarki. Sannan ya kama kan abin haihuwa
ya aske, ya yi sadaka da nauyin gashin da azurfa wanda ya
yayyafe shi da (wani nau’in turare da ake kira da) Khaluk ;
sannan ya sa aka yi masa kaciya.
Wannan abu dai da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi a ranar
sunan Hasan (a.s) ya zamanto sunna da musulmi suke koyi
da ita.
Mnnu//Ng0027
Ma'asumah Nigerian News Update