Biyo bayan hukuncin babbar kotun Nigeria dake birnin tarayya Abuja, wanda tayi na watsi da shari'ar Malamin nasu da nuna rashin yarda a baiwa Jagoran mabiya Mazhabar Ahlil baiti (Shi'a) Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) Passport ɗin shi da gwamnatin Shugaba Buhari ke riƙe dashi tun bayan sakin Jagoran nasu.
Almajiran Shehin Malamin na cikin garin Sokoto sun fito Muzaharar ne domin nuna rashin amince wa da hukuncin kotun, lokaci guda kuma suna kira da Babbar murya a gaggauta sakin fasfo ɗin Jagoran nasu da mai ɗakin shi domin su fita suje neman Lafiya kasan tuwar haryanzu akwai sauran harsasai a cikin jikin Malamin nasu.
—Sidi Khazeem Muhammad
08 Ramadan 1444 (30/3/2023)
#ReleaseZakzakyPassportNow