YANAYI DA LOKUTAN DA YA WAJABA MATAFIYI YAYI AZUMI A CIKINSU .

 


MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATE


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 


A baya mun ambaci cewa baya wajaba akan matafiyi yayi Azumi kuma ko yayi Azuminsa bai inganta ba indai har tafiyar nan takai kilomita 44 , koda kuwa zuwa kilomita 24 dawowa ma haka , to amma akwai wasu halaye da lokuta da yake wajaba akan Matafiyi yayi Azumi a cikinsu su an togacesu daga wannan hukuncin , wanda sune kamar haka :


1. Idan ya zama Tafiyar ta saɓon Allah ce , duk tafiyar da ta zama ta saɓo ce wajibi ne yin Azumi a wannan Tafiyar , kamar wanda ya tafi wani gari don yin sata ko Macen da tafita yin tafiyar ba tare da izinin mijinta ba ko kuma wanda ya tafi yiwa wani Azzalumi aikin zalunci , dukkansu wajibi ne suyi Azumi koda ta haura kilomita 44 .


2. Wanda ya fita bayan Zawali (Azahar) shima wajibi ne ya cigaba da Azuminsa da ya ɗauka , amma kuma wanda ya fita kafin Azahar shi kuma wajibi ne ya ajiye Azuminsa indai ya kai (Al-haddut tarakkhus) .


3. Wanda ya kasance mai yawan tafiye-tafiye ne shi kamar wanda tafiye-tafiye ne sana'arsa irin mai aikin tuƙin Mota da wanda harkokinsa suka dogara akan yawan tafiye-tafiye , shima wajibi ne yayi Azumi .


4 . Wanda yayi niyyar zama a garin da zai je na tsawon kwana Goma ko fiye da haka shima wajibi ne yayi Azumi , amma ƙasa da kwana goma zai yi ƙasaru na Sallah kuma bazai yi Azumi ba .


5. Wanda ya kwashe kwana Talatin a garin da yaje yana tantamar yau ko gobe zai tafi ko zai zauna ko zai koma bai sani ba , tundaga ranar farko da bai yanke shawara ba har ranar 29 duk zai yi ƙasaru a Sallah kuma bazai yi Azumi ba , amma daga sanda ya cika kwana Talatin to wajibi ne ya cika Sallah kuma yayi Azumi .


6. Wanda ya kasance gidansa yana tare dashi ko da yaushe shi bashi da tsayayyen gida shima wajibi yayi Azumi ko a halin tafiya yake , kamar Fulanin tashi (Ƙaura) wajibi ne su cika Azumi .


7. Matafiyin da ya dawo daga tafiya zuwa Garinsa kafin Zawali (Azahar) kuma bai aikata abinda yake karya Azumi ba a hanya kan ya ƙaraso , shima wannan wajibine akansa yayi niyya kuma ya kai Azumin wannan rana matuƙar ya shigo Gari bai ci ko yasha a hanya ba ,  misali .


Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏



9/Ramadhan/1444H - 31/3/2023 Miladiyya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post