WAFATIN SAYYIDUNA ABU ƊALIB (A.S)

 



MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATE


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 



Shugaban Kwarin Makka kuma mataimakin Manzon Allah (Saww) Abu Ɗalib (a.s) ya rasu ne a ranar 26 ga watan Rajab Shekaru uku 3 kafin hijira , ma'ana shekara ta 10 da Aike , dai-dai da shekara ta 619 Miladiyya , a lokacin yana da shekaru tamanin da ɗori .


A wata Riwayar kuma an ce ya yi wafati ne a ranar 27 ga Jumada al-Awwal, ko 29 ga watan Rajab, ko 7 ga watan Ramadan, ko 18 ga watan Ramadan , ko 15 ga Shawwal , ko 17 ga Shawwal , ko farkon watan Zhul - Qa'adah .


Sunansa Abdu Manaf (Imrana) bn Abdil-Muɗɗalib, Mahaifiyarsa kuwa ita ce Fatima bint Amr bn As, kuma shi ɗan uwa ne ga Abdullahi Mahaifin Manzon Allah (Saww ) da Al-Zubair bn Abdil-Muddalib ta wajen uwa da uba , amma sauran ‘ya’yan Abdul Mudɗalib ‘yan uwansu ne daga bangaren uba kawai.


Yayin da Amirul Muminin Ali (a.s) ya faɗawa Manzon Allah (Saww) labarin rasuwar mahaifinsa Abu Ɗalib , sai Manzon Allah yaji baƙin ciki da damuwa da hakan , yace masa : “Ya Ali ! Ka wanke shi, ka yi masa Tahniɗi , kayi masa Ninkafani , Ka sanar dani lokacin da ka ɗora shi a kan Makara .”

Sai Imam Ali (a.s) aikata hakan , sannan Manzon Allah (Saww) yazo kan Gawar Baffansa yana mai jin baƙin cikin rashinsa , sannan ya  ya miƙa masa hannunsa yana mai cewa : “Ya Baffa! Lallai ka sada zumunci kuma ka saka da alkhairi , Ya Baffa , ka raini ƙarami kuma ka taimaki Babba ka ƙarfafeshi .


Bayan wafatin Abi Talib (a.s) Mala'ika Jibrilu (a.s) ya sauka ga Manzon Allah (Saww) yace masa : “Mataimakin ka ya fita daga Duniya , don haka kayi Hijira”.


An karbo daga Imam Muhammad Al-Baqir (a.s) ya ce : “Da za'a ɗora imanin Abu Talib a kan Tafin Sikelin awo ɗaya , a kuma ɗora imanin Halitta baki ɗaya bangaren , da sai Imaninsa ya rinjayi na halitta .


Haka nan Imam BaƘir (a.s) yana cewa : “Shin baku san cewa Amirul Muminina Ali (a.s) ya kasance yana yin  umarni da yin aikin Hajji a madadin Abdullahi da Amina da Abu Talib a rayuwarsa ba ?  Sannan ya yi wasiyya da ayi musu aikin Hajji bayan komawarsa ga Allah .


An ambata cewa Sayyiduna Abu Ɗalib (a.s.) yana daya daga cikin Wasiyyan Annabi Ibrahim da Isma'il (a.s.) , ya kuma kasance Mahardacin Littattafansu ta wannan fuska , Al-Allamatul Majlisi ya yi ishara ga hakan a cikin بحار الأنوار  Juzu'i na 17 Shafi na 142.

Hakan sam ba zai zama abun mamaki ko kokonto ba ga duk wanda ya bibiyi Tarihin Rayuwarsa da kuma yanda ya taimaki Annabi (Saww) a dukkan halaye .


Muna roƙon Allah ya bamu albarkacin Sayyiduna Abu Ɗalib ya kuma tashemu tare dashi da Annabi da iyalansa tsarkaka.


ﺍﻟﺴَّﻼ‌ﻡُ ﻋَﻠَﻴﻚَ ﻳﺎ ﺳَﻴﺪَ ﺍﻟﺒﻄﺤﺎﺀِ ﻭﺍﺑﻦَ ﺭَﺋِﻴﺴِﻬَﺎ، ﺍﻟﺴَّﻼ‌ﻡُ ﻋَﻠَﻴﻚَ ﻳﺎ ﻭﺍﺭِﺙَ ﺍﻟﻜَﻌﺒﺔِ ﺑَﻌﺪَ ﺗَﺄﺳِﻴﺴِﻬﺎ، ﺍﻟﺴَّﻼ‌ﻡُ ﻋَﻠَﻴﻚَ ﻳﺎ ﻛﺎﻓِﻞَ ﺍﻟﺮَّﺳﻮﻝِ ﻭَﻧﺎﺻِﺮَﻩُ، ﺍﻟﺴَّﻼ‌ﻡُ ﻋَﻠَﻴﻚَ ﻳﺎ ﻋَﻢَّ ﺍﻟﻤُﺼﻄَﻔﻰ ﻭﺃَﺑﺎ ﺍﻟﻤُﺮﺗَﻀﻰ، ﺍﻟﺴَّﻼ‌ﻡُ ﻋَﻠَﻴﻚَ ﻳﺎ ﺑﻴﻀَﺔَ ﺍﻟﺒﻠَﺪِ، ﺍﻟﺴَّﻼ‌ﻡُ ﻋَﻠَﻴﻚَ ﺃَﻳﻬَﺎ ﺍﻟﺬّﺍﺏُّ ﻋَﻦِ ﺍﻟﺪِّﻳﻦِ ﻭﺍﻟﺒﺎﺫِﻝُ ﻧَﻔﺴَﻪُ ﻓﻲ‌ ﻧُﺼﺮَﺓِ ﺳَﻴﺪِ ﺍﻟﻤُﺮﺳَﻠﻴﻦَ، ﺍﻟﺴَّﻼ‌ﻡُ ﻋَﻠَﻴﻚَ ﻭﻋَﻠﻰ ﻭَﻟَﺪِﻙَ ﻋَﻠﻲ‌ٍّ ﺃَﻣِﻴﺮِ ﺍﻟﻤُﺆﻣِﻨِﻴﻦَ ﻭﺭَﺣﻤَﺔُ ﺍﻟﻠﻪِ ﻭﺑﺮَﻛﺎﺗُﻪُ.


7/Ramadan/1444H -  29/3/2023 C.E

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post