TUNATARWA:-Shigar da 'Yammata sukayi a gurin Taron daura Aure..



Shigar da 'Yammata sukayi a gurin Taron daura Aure..


shugaban taron ya dubesu yace


Yaa ku Mata duk Abu me Daraja ana bashi kariya ne ta hanyar lullubeshi tayanda ba za a gani ko a taba shi ba👌


1 sai an haqi kasa ake samo azurfa saboda tsabar darajarta


2 Ana hakar lu'u lu'u a tsakiyar teku Dan darajarsa


3 Ana samun zinari ta hanyar hakarsa acikin rami Mai hatsari Dan darajarsa


Mai jawabin yasake kallonsu yace👇


Jikinku Abune Mai daraja na musamman don yafi azurfa da lu'u lu,u da zinari daraja🤏kuma ya kamata ku bashi kariya ta hanyan rufe shi 🙈


Ya sake da cewa idan kuka baiwa jikinku kariya kamar lu,u lu,u da zinari da azurfa to mutane masu daraja da kima ne zasuje neman izinin auranku


Amman idan kuka kasance masu bayana tsaraicinku to mutanen banza da wawaye ne zasu zo Bata Abu Mai daraja. 😭Wanda Allah yai muku baiwa dashi 


Allah ya karemu da iyalinmu daga aikata kowacca irin alfasha... 🤲


                  Mnnu//Ng0027

Ma'asuma Nigerian News Update

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Allah uban giji yasa mudace baki daya.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post