Ci gaba babi na 2
@_Mmaa'asuma Nigerian News Update
Tare da Abokin Aikin Mu
EngMuhammad Hamza UsmanYarsakakea✍️
WAAZINSA DA KARANTARWAR SA
Tarihi ya tabbatar da cewa tun shehu Usmanu yana dan shekara ashirin yafara kiran mutane zuwa ga hanyar Allah. Ana iya gani wannan kamar yadda malam abdullahi ya rubuta a cikin littafinsa maisuna Tazinul. Muna iya raba waazin shehu da karantarwarsa zuwa gida biyu.
NADAYA
majalisarsa ta wa´azi da shiryarwa. Bayani zaizo nan gaba
NABIYU
majalisar koyarwa (ko karantarwa).Acikin wannan zamane shehu kan fita bayan sallar laasar ko bayan sallar isha´i yana fassarawa mutane Alkur anil, yana karantar dasu hadisan manzon allah(s a w) da fikhu da sufanci da uaran fannoni na ilimi. Acikin wadannan darussa nasane yake yiwa mutane bayani, gwargwadon fahimtarsu. darussa nasa sunkasance akan abubuwa biyar. Nadaya bayani akan abubuwan da sharia ta wajabta na daga zahirin shari´a da badininta. Maana dai akan binda ake kira shari`a da hakika. Na biyu: sune darussa akan sunnar Manzo (s a w) da bincikenta da kuma kwadai tarwa daga bin umarninta. Na ukku bincike akan ilimin tauhidi da abinda ake kira ilimul kalami. Acikin wadannan da russane yake gyaran kura kuran da dalibai da marasa fahimta ke kwaftawa wannan fanni. Haka a cikin wannan majalisa ce yakan gabatarda darussa akan fannin fikihu da gyaran hankulan dalibbai dan ganeda wannan fanni da kuma mayar da su zuwaga abinda ya fi zama dai dai. Nahudu sube darussan da yakegabatarwa a gameda gano bubuwa da aka kago a kan jingina ga addini alhali kuwa su ba addini bane. Abin nufi da wadannan su ne bidi o i da al´adu marasa kyawo da aka jingina ga addini . Wannan abu a bayyane yake ga duk wanda ya karanci littafan shwhu kamar su Ih ya`u sunna da Bayanul bidi´a i. karin bayani ga littafansa. Wannan na nuna shehu na da majalisa ta kawra da bidi o i da al adu miyagu. Na biyar sune darussan da yake gabatarwa danganeda ilimin sharia da binciken manyan matsaloli flla filla da kuma ilmantarda dalibai akan manyan matsaloli baki da kawar musu da duk abinda ke damunsu. Wannan na nuni ne ga yadda shehu ke baiwa manyan dalibai ilimi da yadda yake dorasu akan matakan da suka dace dasu. Wadannan sune kadan daga cikin abubuan da shehu ya koyar da dalibansa da masu saurarensa manema ilimi kowane an koyardashi gwargwadon matakinsa. Akan 6angare nabiyu watau majalisar waazi (ta shehu) sarki muhammadu bello yarubuta littafi na musamman mai suna attar jumanu an kaifiyyati.Waazi shaykhu usmanu. Akansa yayi bayanin yadda shehu usmanu ke yin waazi haka kuma yazo da irin wannan bayani a cikin littafinsa na infaku. sarkin musulmi muhammadu bello ya nuna cewa abinda shehu ke bayninsa ga mutane a majalisarsa ta waazai bai shige abubuwa ukku ba. 1.bayani akan asalin addini watau tauhidi.
Aciki wannan darasi ne ya yake bayani bayani akan ilahiyyatu. Bayani akan abubuwan da yakamata ko ya wajaba mutum ya kudurta danganeda kadaita Allah, wanda shine ilahiyyatu. Bayani akan abubuwanda yakamata ko ya wajaba ya kudurta danganeda annabawa da manzanni wannan kuwa shine Nabawiyyatu. Haka kuma da bayanai akan abubuwanda ake ji amma baa ganinsu na daga al amarin lahira kamar bayani gameda wuta da aljanna da suaransu. Wannan kuwa shi ake kira sam iyyatu. shehu usmanu yayi littafi na musamman dangane da wannan sunan littafin kuwa shine Usulu Deen shidai littafin usulu deen littafine karami (ga takardu) ammayakunshi duk abindabukata gameda tauhidi. Acikin wannan majalisin shehu yayibayanin siffofin da suka wajaba a siffanta allah da su na daga samuwarsa da dadewarsa da wanzuwar sa har zuwa karshensu.Yakan ce dukan Halitta duka fararrace kuma ma haliccinta Allah. Yakance "MALA' IKU" dukansu tsararrune basu sa6a wa `Allah´ ga abinda ya umarce su kuma suna aikata abinda ya umarcesu. su halitta ce mai haske su ba maza kuma ba mata ba; ba su ci kuma basu DAYA Sa annan duk abinda yashafi ubangiji yayi bayaninsa. Hakama yayi bayani akan abinda yashafi annabawa; da abinda yashafi ranar Alkiyama Haka kuma kowace matsala tundaga siffofinda suka can canci a siffanta ubangiji dasu har zuwa bayanin lahir, kowace matsala saida ya ambaci hujjarta daga alqurani Maigirma. Adubi littafin Ihyau sunna nasa a babin imani. Haka kuma ana iya duba infaku da tar juman dukansu na sarkin musulmi muhammadu bello. Ana ma iya duba littafin Usulu deen. Abu nabiyu da yake bayani akansa a irin wannan majalisa ta waazi ga masu karamin sani, shine fannin furu´a watau dai Fikihu. Acikin wannana fannin shehu na karantarda masu sararensa alwala da yadda ake yinta. yana kuma koyar da su wanka da yadda ake yinsa. kuma yana koyardasu taimama dayadda ake yinta. Bayan haka kuma sai yashiga bayani akan sallah tare d yimasu bayanin siffar yadda ake yinta. Sa`annan sai yayi masu bayani a kan sujadar rafkanuwa. Bayan haka, sai yayi bayani akkan zakka da matsayinta da nau o inta har zuwa zakkar fidda kai. Bayan haka sai bayani kan azumi da hajji da yanka da hukunce hukunce rantsuwa da alkawari, haka kuma yatabo hukunce hukuncen aure da ciniki. Abin nufi shine shehu yanada majalisar da yake yiwa masu saurarensa bayani akan abubuwan da suka gabata daga lokaci zuwa lokaci. Awani lokaci yayi bayani akan sallah. awan lokaci yayi bayani kan aure awani lokaci yayi bayani akan ciniki. Da wannan ne zamu gane cewa dolene mai waazi yazama yana tabo kowane sashi awajen waain sa. Bawai matsala guda koyaushe tazama abin tattaunwa ba. Wani abu kuma da shehu kan yi magana akansa wanda yake shine abu na ukku da yakan tattauna akansa kuma yayi bayni ga masu sauararensa, shine fannin sufanci . Acikin irin wannan majalisa ce shehu kan cewa masu saurarensa, Yana wajaba a kan kowane musulmi da ya tsare kunnuwansa ga sauraren kowane magana ta wasa da batsa kuma yatsare ida nunsa ga duban abinda yake haram. kuma ya kiyaye harshensa ga fadar giba da dukkan abinda bai halattaba. Haka kuma yatsare hannunsa daga sata da dukan abinda baa yarje masaba da ya aikata ba. Haka kuma yakiyaye cikinsa daga sanya masa haram kuma yakiyaye al aurar sa daga zina da liwadi. Yakiyaye kafafunsa daga tafiya irinta takama da zuwa wurin sabo. Wadannan sune gabbai guda bakwai wadanda idan mutum yakiyayesu to yazama mutum salihi nagari. Acikin irin wannan majalisa ce har wayau dai shehu ke karantarda masu saurare siffofi na munjiyatu watau siffofi masu ku6utarwa kuma masu tseratarwa ga shiga wuta .Haka kuma yanayimasu bayanin muhlikatu watau siffofi masu halakarwa kuma su sanya mutum wuta. Munjiyatu sun kunshi tuba da ikhlasi da hakuri da gudun duniya harma kuma ga dogara ga allah da fauwala al amari zuwa gareshi .
Zamuci gaba in sha Allah ku kasance tare da mu a Shafin mu na Ma'asuma Nigerian News Update
Real Naseer Umar Alhassan
Na Shaheeda Bawan Allah
2/9/1444. 24/3/2023