Shaikh Zakzaky (H) Ya Tunatar Dangane Da Ayyukan Watan Zul-hijjah.

 



Sidi Abba A Aliyu .MNU44


Shaikh din ya yi wannan tunatarwar ce a ranar Laraba, 30 ga watan Zulkada, 1435 (24/9/2014) jim kadan da kammala Tafsirin Alkur’ani mai girma da aka saba gudanarwa a duk ranar Laraba a muhallin Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya. Ammar Muhammad Rajab ya rubuta muku. Ga Jawabin kamar haka: 


Shekaran jiya na yi wani kuskure, na ce muku ainihin wata 29 zai yi. Dalili, na duba ne na ga shi watan in har Zulkada zai tafi daidai, to ya nuna 29 ne. Sai daga baya da naje na duba sai na ga ya sa 29 din ranar Laraba ne, an fahimta ai? Saboda haka lallai, yau dai 30 ne a lisssafinmu, mu a namu 30 ne yau! Saboda haka ko ya zama 29 a gareka ko 30, yau ne  karshen wata.


Saboda haka abin da na fadi wancan Litinin din, lallai na yi kuskure, daga baya na gano kuskuren, amma da muka je shan ruwa, na gaya ma wasu cewa; na duba na ga cewa na yi kuskure. Domin dalili, shi ya nuna min 29 ne karshen watan, ashe Laraba ya sa. Ko ba a lura ba? Saboda haka Laraba ne karshen wata (yau ne kuma Laraba). To, yau Laraba, shi ne karshen wata. Ko ya zama a lissafinka 29 ne ko kuma ya zama 30. 


Idan a Saudi Arebiya, yau sun ce an ga wata, don su a lissafin su yau 29 ne, to gobe daya ga wata, zai zama ainihin ARFA za ta fado ranar Juma’a, sallah kuma ta kasamce ranar Asabar. Idan suka ce ba a gani ba, don muna da labarin cewa; sukan ji tsoron ARFA ranar Juma’a. Dan an ce Sarki kan mutu ne in aka yi. Idan Sarki ya mutu sai su duba sai suka ga cewa; wannan Shekarar ARFA ta fado ran Juma’a ne. Saboda haka da zarar an ce ARFA ta fado ran Juma’a, Sarki zai ce; ko wannan shekarar ne za a tafi? Ko kuma sai wata kuma? Saboda haka sukan so su kauce ma ARFA  ya fado ran Juma’a.


Akwai wata shekara da na tafi Hajji, sai ya zama muna Madina 29 ga watan Zulkada, to, sai wata ya tsaya ya yi banbaro ya dade, ba yadda za a yi mutum ya ce ba a ga wata ba, to, dole dai suka bari aka yi ARFA din ranar Juma’a. 


To, kuma mutane su kan ta hankoro su je Hajji idan ARFA ta fado ran Juma’a an fi cika. To, ko ya zama sun ce Arfa ran Juma’a ne ko su ce Asabat ne, to mu dai ainihin ranar Asabat ne ranar Sallah, an fahimta ai? Yawwa!  


Ranar Asabar rannan ne ranar sallah. Saboda haka ainihin ko ya ya lissafin Saudi Arebiya ya kama, kuma tana iya yiwuwa ya zama ‘genuinely’ ba su ga watan ba ne, dan lissafin su yau 29 ne, tana yiwuwa su kuma ya zama ba su ga wata ba, su cika watan, babu laifi in suka yi haka nan. 


In ka je Hajji sai ka yi lissafin su a can, an fahimta ai? Amma mu a nan, gobe 1 ga wata! An fahimta? Gobe Alhamis zai zama daidai da 1 ga wata. 


Zulhijjah yana da ayyuka mai yawa, in mutum yana so ya duba cikin Mafatihu akwai jagora. Wannan kwana goman farko din nan su ne; ‘layalil ashir’ din nan na ‘wal fajri’ ‘wal fajri, wa layalil ashir’, wanda Allah (T) ya rantse da wadannan, darare ne masu daraja, ayyuka a cikin su na da lada mai yawan gaske. 


To, kuma ana azumtar wadannan kwana tara din. Domin wanda ya yi azumin kwana 9 din nan, kamar ya yi duk rayuwarsa azumi kawai yake yi. Wato ladarsa zai zama kamar wanda gaba daya rana duk yana azumi ne. 


To, sannan kuma akwai wasu salloli da ake yi da wasu addu’o’i, insha Allah ba sai na karanto muku ba. Wannan idan mutum ya duba zai ga Mafatihu, ya ce; na 1 na 2 na 3 duk ya kakkawo su, addu’o’i daban-daban. 


Sannan kuma musamman azumin ranar ARFA, wanda aka ce ainihin shi azumin ranar ARFA din. ARFA a wurinmu shi ne; ba ranar da aka tsaya ARFA a Saudi Arebiya ba. Ranar 9 ga wata. Ko da rannan mu sallah muke yi a rannan, mu muna iya yin sallar mu rannan (ranar ARFA din Saudi Arebiya). 


Kamar bayanin da na yi. Ba ruwanka, in dai ya tabbata mu 1 ga wata ne a nan, 2 ga wata, ranar 9 ga wata , rannan ne tara. Ba ruwanka da ko rannan ne 8 a Saudi Arebiya. Da na ku zaka yi lissafi. 


Amma idan kaje Makkah kai aiki da na Makkah can. To, shi wannan azuminsa ya fi lada (na ranar ARFA). 


Insha Allah, da yake muna da lokaci na kawo wannan. Ainihin dai yana da kyau dai mutum ya ai azumin wadannan kwanaki tara din. 


Sannan har wala yau, lallai wajibi ne cikin wajibobin addini, idan kana da hali, dole ka yi layya. Halin shi ne; ba kana da Rago yana cewa; ‘mee’ ba. Idan kana da abin Rago kana da Rago. Ko kana da wata babbar Riga, kwado da Linzami, aska biyu, ba ka sawa, idan kudin ta ya kai daidai Rago, to Rago ne! Yawwa! Ko kana da wani abin da ka ajiye, wani Agogo da baka sa shi, ba dole ne a sa ba kuma in dai aka ganganda aka ganganda za su yi Rago, to, kana da Rago.


Ba sai kana da kudin Rago ko kana da Rago yana ‘mee’ ba, idan kana da abin kudin Rago, to kana da Rago, kuma wajibi ne ka yi. Duk lokacin da layya ya zo kana da hali, wajibi ne ka yi. Sai dai idan baka da hali, ba a ce ka matsa ma kanka ba. Ba a ce ka ci bashi ka yi ba. an fahimta ai? Idan kana da hali ne ya zama wajibi! 


Sannan kuma ana son wanda zai yi layya, wadannan kwanaki goma din nan, har sai bayan idan ya yi layya, ana son ka da ya yanke farce, farce da Sakkwatanci, yatsa ke nan ko? Kar ya yanke Akaifa. Ba a yanke Akaifu, ba a aski. Amma iyakan abin da aka ce ke nan. Ba a ce kar ya bulbula turare ko kar ya yi kaza ba, ba a ce ya yi ‘i’itizami’ da ka’idodin mai ‘IHRAMI’ ba, illa iyaka wadannan abubuwan ne kawai aka ce kar ya yi. Ya bar gashin kansa, kar kuma ya cire Akaifu a kwanakin nan goma, har sai ya yi layya, sannan sai yana iya yin wannan (aski da yanke akaifu). 


To, kuma dai da wadansu abubuwa da suka shafi, amma ba a ce kuma kar ya yi wadansu abubuwa ba. Ba a ce zai yi ‘i’itizami’ da ayyukan mai ‘IHRAMI’ ba ne. To, insha Allah. 


Wasallahu Ala Muhammadin wa’alihid Dahirin.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post