SAI WAƊANNAN SHARUƊƊAN SUN HAƊU SANNAN AZUMI YAKE WAJABA AKAN MUTUM KO YA INGANTA GARESHI !!!

 


MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATE


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 


Waɗannan sharuɗɗan da za mu zayyano sune sharuɗɗan ingancin Azumi ko wajabcinsa akan Mukallafi , in basu haɗu ba ko mutum yayi Azumi to baya inganta ko ba wajibi bane akansa yayi , sharuɗɗan sune kamar haka :


1. Musulunci , Azumin Kafiri baya inganta ko da yayi , duk da cewa wajibi ne akansa yin Azumin amma kuma ko yayi bai inganta ba a bisa ra'ayin mafi yawan Malaman Shi'a Imamiyya.


2. Imani , duk da wasu Malamai suka ce : Imani ba sharaɗin inganci bane sharaɗi ne na cancantar lada da karɓar aiki ba wai sharaɗin sarayar Taklifi akan Mukallafi ba .


3. Rashin wayar gari a halin janaba ko halin Haidha ko jinin biƙi (Jinin Haihuwa) , duk wanda ya wayi gari da ɗaya da cikin waɗannan Azuminsa baya inganta , bari ma baya wajaba akan mai Haidha da Jinin Haihuwa yin Azumi .


4. Kar ya kasance a halin tafiyar da take wajabta yin ƙasaru a Sallah , wacce takai nisan (44km , koda zuwa 24 dawowa ma 24 ne , wannan sharaɗi ne na wajabci da ingancin Azumi .


5 . Balaga , Azumi baya wajaba akan Namiji sai ya kammala shekara goma sha biyar (15) a Lissafin wata , Mace kuma sai ta cika shekara tara 9 a bisa zance mafi shahara a wajen Malamai .


6 . Hankali , don haka Azumi baya wajaba akan wanda ya rasa hankalinsa (Mahaukaci) .


7. Rashin suma , wanda ya kasance a cikin halin suma Azumi baya wajaba kuma baya inganta gareshi , da ace mutum zai haukace ko ya suma ta yanda Niyyar Azumi ta suɓuce masa bai yi ta ba , to idan ya farka ko ya watssake da rana baya inganta yayi Azumin wannan ranar tunda bai riga da yayi niyya ba .


8. Lafiya , Azumin mara lafiya baya inganta in ya zamanto yin Azumin zai cutar dashi ko ya ƙara masa rashin lafiya ko ya jawo masa jinkirin warkewa , kuma ko da zato yake yi ba wai sai yaƙini (sakankancewa) ba , haka nan in yayi tantamar da suke da madogarar hankali .


Shima mai lafiya in yaji tsoron cutuwa da yin Azumi ko yasan cewa in yayi zai cutar dashi baya inganta gareshi yayi , shi ko mara lafiyan da ba zai cutu ba in yayi Azumi yana inganta gareshi yayi kuma wajibi ne akansa yayin .


9 . Kar ya zama ana binsa Azumin Wajibi amma ga wanda zai yi Azumin Nafila kenan , domin ba'a yin Azumin Nafila ga wanda ake binsa Azumin Wajibi kamar Ramadan.


Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏


8/Ramadhan/1444H - 30/3/2023 .

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post