-WANENE ABU ƊALIB (RTA)?
-Abu-Ɗalib, Shine Mahaifin Imam Ali (AS), Ainashin Sunan Abu Ɗalib Shine (Imran) Ko Kuma Abdul Manaf, to Amma An fi Saninsa da Wannan Suna na Abu-Ɗalib, Hakan Kuwa Lakabi Ne Ake yi Masa da Babban 'Ɗansa Mai Suna Ɗalib.
-Shi dai Abu Ɗalib Baffa Yake ga Manzon Allah (S) Don shi Ɗan uwa Ne Shakiki ga Abdullahi Baban Annabi (S).
-Kuma Shine Ya Cigaba da Kulawa da Annabi (S) Har Zuwa Girmansa Bayan Rasuwar Mahaifinsa Abdullahi da Kuma Kakansa Abdul Mutallib.
-Lalle Tarihi Ya Tabbatar Mana irin Tsananin Ƙauna da Soyayya da Kuma Kulawan da Abu Ɗalib Yake Nunawa Ma’aiki (S) Sama da Yadda Yake Nunawa Ƴa’yansa
-Haka Nan Kuma Bayan Girmansa da Kuma Lokacin da Aka Aiko shi A Matsayin Annabi, Ya Cigaba da Kare shi, Bayan Yayi Imani Dashi, Har Lokacin da Allah Ya Karbi ransa, Ya koma ga Rahamar Ubangiji.
-Nasabarsa; Abu Talib: Shine Dan Abdul Mudallib, Dan Abdu -Manaf, Dan Qusayyu, Dan Kilab, Dan Murra, Dan Ka'abu, Dan Lu'ayyu, Dan Galibu, dan Fihru, Dan Maliku, Dan Nadar, Dan Kinanatu, Dan Huzaimatu, Dan Mudrikatu, Dan Ilyasu, Dan Mudar, Dan Nazar, Dan Mu'addu, Dan Adnan, Dan Adad, Dan Addi, Dan Humaisa'u, Dan Qaidaru, Dan Annabi Isma'il (AS).
-Dan Annabi Ibarahim (AS), Dan Tarakha, Dan Nahuru, Dan Sarugu, Dan Arugu, Dan Faligu, Dan Abiru, Dan Shalikhu, Dan Arfakhashadu, Dan Samu, Dan Annabi Nuhu (AS).
-Dan Lamaku, Dan Matushalakhu, Dan Akhanukhu, Dan Yaridu, Dan Mahlailu, Dan Qainanu, Dan Anushu, Dan Shisu, Dan Annabi Adam (as).
-To Malam, Kaji Dangantakar Abu Talib (as) Har Zuwa Annabi Adam (as) duk Kakannin Nasa daga Annabi sai wasiyyin Annabi, Ko Waliyyi daga cikin Waliyyan Allah (swt), Kuma Wannan dangantakar itace Dangantakar Annabi Muhammad (S) da Imam Ali (as).
-An haifi Abu Talib a Makkah, shekara 35 Kafin Shekarar giwa. kenan Ya girmi Annabi (S) da Shekara 35. 535 M.
-Abu Talib (as) Yana da Mata guda 1; Fatimah bint Asad (as) da 'Ya'ya biyar Sune:
-(1) Talib Wanda ake Masa Alkunya dashi.
-(2) Aqeel Mahaifin Muslim bin Aqeel; Dan aiken Imam Husain (as) a Kufa.
-(3) Ja'afar Wanda Ya Jagoranci Hijira Zuwa Habasha, an fi Saninsa da At tayyar.
-(4) Imam Ali (as) Khalifan Manzon Allah (S) Na 4 a Wajen Ahlus Sunnah. Na farko a wajen Shi'a.
-(5) Fakhitah Ummu-
Hani: Wacce Annabi (S) Yayi Isra'i daga Dakinta.
-Wani abin Mamaki Shine, dukkan 'Ya'yan Abu Talib biyar, Shekara 10 ne tsakaninsu.
-Abu Talib Yayi fice a Tsakanin Larabawa Saboda Kula da Dakin Ka'aba da Shayar da Al-hazai Imaratul-masjidul-haram/Siqayat al-Haj.
-Abu-Dalib Yayi Wafati a 26 ga Watan Rajab, Shekara 3 kafin Hijira, 619 M, Kafin Isra'i da Miraji, har lokacin da Abu Talib (as) Ya Rasu, Yin Sallah biyar ko Wace Rana bata Zama Wajibi ba, domin a lokacin Babban Nauyin da Ya doru a kan Manzon Allah (S) Shine Ya Kira Mutane Suyi furuci da Kalmar Shahada, amma batun Sallah babu Wani labari akai.
-Daga cikin gudunmawar da Abu Talib (as) Ya bawa Annabi (S) Shine; Abu Talib (as) Ya aurar da Annabi (S) Kuma Ya bawa Nana Khadeeja (as) Rakumi 20 a Matsayin Sadakin auren Annabi (S) Kuma Yayi Huduba da Sunan Allah a
Wajen auren.
-Saboda Kare Annabi (S) Abu Talib (as) Ya Shiga Cikin Kuncin Rayuwa, har hakan Yayi Sanadiyar Wafatinsa.
-Annabi (S) Ya kiran Shekarar da Abu Talib (as) Yayi wafati da Shekarar bakin Ciki, Saboda Ya rasa Babban Mai bashi Kariya.
-An Ruwaito Annabi (S) Yana Cewa; "Ba don Kariya ta Abu Talib (as) ba, da Kuma dukiyar Khadijah (as) da takobin Imam Ali (as) ba, da Wannan addini bai tsaya da kafarsa ba".
-Musulunci ya tsaya da Kafarsa ne Saboda Kariya irinta Abu Talib (as) dukiyar Khadijah (as) da Kuma Takobin Imam Ali (as).
-An binne Abu Talib (as) a Makabatar Jannatul-Mu'alla, (makabarta Al Hajun) (Al-Hajun Cemetery).
-Rashin Abu Talib (as) ne Yasa Annabi (S) Yayi Hijira daga Makka zuwa Madinah.
-Wannan kenan a takaice dangane da tarihin Sayyadi Abu-Dalib (as).
-'Yan uwa don Karin Bayani Sai ku duba Wadannan Littattafan.
-1. Al-Ya'qubi, j2, s14; Qumi, j1, s108-9.
-2. Al-Baladhuri, j 2, s 288.
-3. Al-Halabi, j 1, s 184.
-4. Ibn Sa'd, j 1, s 119.
-5. Ibn Kathir, j 3, s 164....
-Muhammad Jiddah Nguru
07037009525