MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATE
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
Ba duk wanda ya yabi Ahlul baiti (a.s) bane ya zama ɗan Shi'a , Su Ahlul baiti har maƙiyansu ma suna yabon su saboda girma da matsayinsu, akwai waɗanda ba Musulmi bane amma sun rubuta Kundayen ƙasidun yabon Ahlul baiti (a.s) da ko a cikin Musulmin sai an jinjina kan a samu mai irinsu , a Kasar Iraqi anyi Abdul raq Abdul Wahid wanda ɗan Addinin Sabi'anci ne amma in yana yabon Ahlul baiti ko ƴan Shi'ar ma sallama masa suke wajen iya zuba baituka , don haka ba iya yabo bane Shi'anci .
Haka nan ba duk wanda ya faɗi Falalar Ahlul Baiti bane ɗan Shi'a , domin su Ahlul Baiti (a.s) har maƙiyansu suna faɗar falalarsu , akwai Malaman da suka shahara wajen gaba da ƙiyayya ga Ahlul baiti amma kuma Litattafansu cike suke da Hadisai da bayanin falalar Ahlul baitin , dama cikar falala shine a jita daga wajen maƙiyi , kuma har wanda ba Musulmi ba suna faɗar falalarsu , littafin " The Voice Human Justice " ya isheka misali wanda George Jordac ya rubutashi , kuma akwai tarin Littattafai akan falalar Ahlul baiti (a.s) waɗanda Masallatansu ba Musulmi bane .
Nasu magana sukance Falala itace abinda maƙiya suka bada sheda dashi (الفضل ما شهد به الأعداء) , hatta Mu'awiyah da ya yaƙi Imam Ali (a.s) in ya keɓe da wasu mutanensa yana faɗa musu falalar Imam Ali kuma ya faɗa musu Ali ya fishi.
Haka nan ba duk wanda yace yana son Ahlul baiti (a.s) bane ya zama ɗan Shi'a , domin sonsu wajibi ne akan dukkan Musulmi kamar yanda yazo a ciin Alkur'ani :
قُلْ لَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْرًا إِلَّا الْمَوَدَّةَ فِي الْقُرْبَى [الشورى: 23] .
Sannan akwai dayawan waɗamda ba Musulmi ba amma suna matuƙar ƙaunar Ahlul baiti (a.s) ko za ka samu Ahlul baiti suna birgesu matuƙa , kuma wannan ba abun mamaki bane Ala sabilil misali za ka samu dayawan Musulmi suna ƙaumar wani shahararren ɗan Ƙwallon ƙafa ko ɗan dambe ko ɗan kokawa kuma yana birgesu sosai amma kuma shi ba Musulmi bane , hakan baya nuna lallai sun koma Addininsa .
Shi yasa in ana manyan taruka a kasar Iraqi ko Iran za ka ga har wanda ba Musulmi ba kamar Kirista da Sabi'awa da Izidiyawa suna kawo Ziyarar ban girma da nuna ƙauna ga Ahlul baiti (a.s) , kenan ba nuna ƙauna ga Ahlul baiti (a.s) kawai bane Shi'anci, to menene ne Shi'anci ???
AMSA : Mutum baya zama ɗan Shi'a Imamiyya har sai ya kasance mai ƙudirce wasu Rukunai , bayan Imani da Allah (Tauhidi) da Annabta da Alkur'ani , Rukunan kuwa sune kamar haka :
1. Wajibi ne ya ƙudirce cewa Manzon Allah (saww) ya sanya Imam Ali (a.s) - da umarnin Allah - ya zama shine Imami a bayansa tun a rayuwarsa da bayyanannen Nassi , kuma duk wanda yayi watsi da hakan babu shakka yayi watsi da wani rukuni daga cikin rukunan Addini .
2. Ƙudirce cewa Manzon Allah (Saww) ya Nassanta Imam Hassan da Imam Hussain (a.s) a matsayin Imamai kuma jagororin Addini a bayan mahaifinsu Imam Ali (a.s) kuma shima mahaifinsu yayi bayanin hakan a ƙarara .
3. Ƙudirce ci gaban Imamanci a cikin zuriyar Imam Hussain (a.s) daga Banu Hashim har zuwa ranar Alƙiyama .
4. Wajibi ne Ƙudirce adadin Imamai Goma sha biyu ne babu ragi babu ƙari, Tara daga cikinsu daga zuriyar Imam Hussain (a.s) suke kawai .
5. Ƙudirce cewa babu wani zamani da lokaci da zai zama babu wani Imami daga cikin Imaman nan sha biyu za kuma na ƙarshensu shine Imam Mahdi Al-muntazar (a.s) da yake a raye abun azurtawa, sannan zai bayyana duk sanda Allah yaso don ya cika ƙasa da Adalci da daidaito bayan an cikata da zalunci .
6. Ƙudirce kasancewar Imami Ma'asumi ne daga dukkan saɓo da kuskure da zamiya , kuma Allah ya sanar dashi dukkanin iliman Addini tare da yi masa baiwa da cikar falalar da bai yiwa wani a mutanen zaminsa ba .
7. Wajibine miƙa wuya da Sallamawa waɗannan Imamai cikin umarni da hane-hanensu tare da wajabcin binsu da ƙaunarsu gami da wajabcin yin Bara'a (Baram-baram) da maƙiyansu .
In waɗannan rukunan basu haɗu a cikin Aƙidar Mutum ba bai zama ɗan Shi'a Imamiyya ba .
Duk wanda ya yabi Ahlul baiti (a.s) ko yake da'awar ƙaunarsu tare da faɗar falalarsu , idan Musulmi ne mafi kyawun abinda za ka siffantashi dashi shine ya sauke wani yanki na wajibin da yake kansa a Shari'ar Musulunci na wajabcin ƙaunarsu , in kuma ba Musulmi bane ba komai Soyayyarsa ke nunawa ba face girma da matsayin Ahlul baiti (a.s) , ta yanda hatta wanda ba Musulmi ba ya sheda da Insaniyyarsu da matsayinsu shi yasa ya yabesu .
Don haka ya kai wanda yake jingina Mutane da Shi'anci don sun yabi Ahlul baiti (a.s) ko sun yabesu ka sani ba wannan bane kawai ainihin Shi'anci , akwai wasu rukunai da sai sun samu a cikin Aƙidarsa ake kiransa ɗan Shi'a .
Kaima ɗan Shi'a ka dena rawar ƙafa da azarbabin kiran mutum ɗan Shi'a natuƙar bai ƙudurce rukunan zama ɗan Shi'a ba , don mutum yayiwa Shi'anci adalci a wata mas'ala ko ya faɗi gaskiya baya nufin ya zama ɗan Shi'a , wata ƙila kafin ya yabi Shi'anci sau ɗaya ya shafe shekaru yana sukar Shi'anci, musamman in ya zama adalci ne na ɗan Boko ko mutum mai neman suna da maslaha , idan suka samu abinda suke so a wurinka gobe za ka iya hindu suna faɗa da Shi'ancin.
Ba wai ina suka ko aibanta wanda suke yabon Ahlul baiti (a.s) bane daga wajen Shi'anci , ko ina kokonton kyawun niyyarsu da gaskiyarsu a cikin da'awa da abinda suke yi bane , ko shakka babu a cikin gaskiyar niyyarsu da nufinsu, kuma hakan abun alfahari ne musamman a wannan zamani da bayyana ƙaunarsu ko yin yabonsu ya zama abun gudu don kar a jinjinawa Mutum Shi'anci, Madallah da Sabi'anci kuma Madallah da Ƴan Shi'a.
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏
9/Ramadan/1444H - 31/3/2023 Miladiyya.