Daga Ibrahim Al-mustapha Saminaka.
Jagoran Harkar Musulunci A Najeriya Sheikh Ibraheem Yaqoub Al-Zakzaky ya raba kayan abinci ga mabuƙata kamar yanda ya saba kowace shekara.”
“An raba kayan abincin ne a yau Laraba 29 ga watan Maris, 2022. Kayan abincin da aka raba sun hada da shinkafa, Dawa, Masara, Gero da sauran su. A karshe Shehin Malamin yayi fatan alkairi ga dukkan al'ummar Musulmi.”
Bugu da ƙari kamar yadda muka wallafa hakan a sama cewa; jagoran Harkan Musuluncin a Najeriya wato Sheikh Ibrahim Zakzaky ya saba wannan al'amari a duk Shekara, kama har lokacin da yake tsare a hannun gwamantin Najeriya bai daina wannan aikinba na Rabawa Mabuƙata kayan hatsi rigis a duk Shekara musamman a cikin watan Ramadan.