Ra'ayin Mallam Zakzaky Akan Mata.

 



@_Ma'asumah Nigeria News Update

   // Mnnu/Ng0041


— Baqerul Hakeem


A ra'ayin Mallam Zakzaky sam bai yarda a maida mata kayan gida ko bayin cikin gida ko masu zaman dirsham na hidimar mazajensu a gidajensu kawai ba, Mallam Zakzaky yana ganin mata na taka muhimmiyar gagarumar gudunmawar cigabantar da al’umma ne, ta hanyar zuwa da su fagen addini da yin sa’ayi wajen neman yardar Allah da gwagwarmayar ceto wannan al'umma.


Mallam Zakzaky, yana ganin girmama mata tare da basu dukkan haƙƙoƙinsu yana daga cikin babban abin da wannan al’ummar take buƙata a wannan lokacin, kuma zai warware tarin matsaloli da rashin samun cigaba da jefa al’umma cikin halin cibaya da suka tsinci kawukansu, al'umma na buƙatar gudumawar mata sosai da sosai domin bunƙasa Yau da Gobensu.


Mallam Zakzaky yana yawan kira a bawa mata damammakin zuwa makaranta da shiga lamarin zamankewa domin bada gagarumin gudummawa ga wannan al'umma, Mallam Zakzaky na daraja mace tare tausayinta sosan gaske!


Mallam yana ganin rashin ba mata damammaki tare da wofantar da al’amarinsu, da takaita su da kayan gida kawai yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka jefa ƙasar nan cikin hali na cibaya.


— Baqerul Hakeem.

—22/08/1444H (14/03/1/2023).

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post