MUTANEN DA SHARI'A TAYIWA RANGWAME SU SHA AZUMI

 


Shari'a tayi rangwame ga wasu mutane su sha Azumi (Baya wajaba a kansu suyi Azumi ) daga cikin waɗannan mutanen akwai : 


1. Tsoho da Tsohowa da mai cutar ƙishirwa idan yin Azumi ya gagara garesu ba za su iya ba , ko yin zai jawo musu wahala mai tsanani to anan Shari'a ta musu rangwame ba sai sunyi Azumi ba , amma kuma za su bada "Fidya" ga kowacce rana gwargwadon Mudu ɗaya na abinci wato (gram 750) kullum , kuma baya wajaba akansu su rama ko da sun samu damar ramawa daga baya duk da Mustahabbi ne su rama ɗin in sun samu dama amma ba dole bane , haka nan Mustahabbi ne ya zama sun bada Mudu biyu kullum maimakon Mudu ɗaya kuma ya zamanto abincin daga Alkama ne (amma ba dole bane).


2. Mai cikin da ta kusa sauka idan yin Azumi zai cutar da ita ko ya cutar da ɗan dake cikinta itama an mata rangwame ta sauke Azumi.


3. Da Mai shayarwar da take da ƙarancin ruwan Mama idan Aikin zai cutar da ita ko ya cutar da ɗanta , itama am mata rangwame .


Sai dai da Mai cikin da Mai shayarwar dukkansu za su rama daga baya sannan kuma akwai "Fidya" irinta Tsoho da Tsohowa da mai ciwon ƙishi akansu .


TAMBIHI 


Dangane da mai Shayarwa ba dole sai ya zama ɗanta na cikinta ba aka yi mata rangwame , hatta dan da ba nata ba indai ita take shayar dashi ta shiga cikin hukuncin da aka ambata , amma bisa Ihtiyaɗi ya zamanto iya ita kaɗai ce za ta iya shayarwar ta yanda ya zama babu wata hanya da za'a iya shayar da yaron ko da kuwa ta hanyar haɗa masa da wani abu kamar abinci (ba tare da wani abu da zai hana ba ) , ko kuma Shayarwa ta wucin gadi in zata samu , inko ba haka ba baya halatta gareta ta ƙi yin Azumi .


وصلى الله على محمد وآله الطيبين الطاهرين


Kar ku manta mu a cikin Addu'oinku masu albarka da daraja .


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 

 

2 /Ramadhan/1443H - 24/3/2023 Miladiyya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post