(1)
Idan mutum yayi bincike Addu’a a
mahanga ta Ahlul bayt wato a bisa karantarwa
ta Ahlul bayt zai ga cewa Addu’oin da aka samo
daga Aimma na Ahlul bayt babu wani da aka
samo irinsu a wannan al’umma ta Manzon Allah
[S] wannan a bayyane yake duk wanda yayi
bincike zai ga haka misali mutum ya kwatanta
littafan Addu’oi da ake dasu a Shia da kuma
Sunna,wato zai ga cewa littafan Addu’oi a Shia
sun fi yawa kan na sunna,in mutum yayi tunani
zai ga cewa }ila wannan bai rasa nasaba da irin
halin da Aimma da kuma shi’arsu suka kasance
na jarabawowi dabam dabam tsakaninsu da
hukumomi da kuma jama’a na
zamunnansu.Saboda haka duk wanda yake
riyawar cewa yana bin Aimma na Ahlul bayt
amma yaga babu wata jarabawa da yake fuskanta
to ya binciki kansa ko dai ba tafarkinsu yake
biba.Saboda dukkan Aimma da mabiyansu sun
sha wahala an kuma cutar dasu ta fuskoki
dabam dabam,kai baki ]ayansu daga wanda aka
kashe sai wanda aka sa ma guba,kuma mutum
ya tambayi kansa idan Imam Mahdi[AF] ya
bayyana Gwagwarmaya zai yi domin tabbatar da
Addini ko zama zai yi ya ba da karatu shike nan?
Mu kuma duba tarihin Imam Khumaini yayi
gwagwamarya domin tabbatar da Addini ya
kuma ba da karatu.
Idan mutum ya bibiyi littafan Addu’oi zai
ga cewa addu’oi sun kasu kashi hu]u sune:
1-Na yaumiyya wato wa]anda ake karantawa
kowace rana,misali na safe da yamma ko na
bayan salloli da dai sauransu.
2-Na Usbu’iyya wato wa]anda ake karantawa
kowace rana cikin mako,misali na ranar
Jumma’a,Asabar,Lahadi……
Za'a cigaba insha allah
Mnn//Ng0027
Ma'asumah Nigerian News Update