(2)
3-Shahariyya wato wa]anda ake karantawa
kowane wata misali daren farko ko ranar farko
na wata, da kuma kowace rana a cikin wata
kamar ranar 1,2,3,har ya zuwa 30 ga wata.
4-Sanawiyya wato wa]anda ake karantawa
kowace shekara misali Addu’ar Ummi Dawud ko
yaumul-mab’as ko Addu’ar sha’abaniyya ko
Addu’oin watan Ramadan wato wanda in mutum
yayi su sai kuma wani watan Ramadan.To ana so
mutum ya dunga bibiyar wannan nizami na
Addu’oi a rayuwarsa.Akwai malamai da suka
rubuta littafai na Addu’oi kan kowanne daga
cikin kashi hu]u na Addu’in da aka
ambata,misali littafin Falahis-Sa’il addu’oin dake
ciki baki ]aya na Yaumiyya ne.Akwai kuma
littafin Jamalul-Usbu’i shi kuma Addu’oin dake
ciki duka na mako ne.Akwai kuma littafin
Duru’ul waqiya shi kuma Addu’oin dake ciki
baki ]aya na Wata ne.Akwai kuma littafin Iqbal
shi kuma Addu’oin dake ciki duka na Shekara
ne.Saboda haka idan zai yiyu yana da kyau
mutum ya mallaki wa]annan littafan domin
lizimtar wa]annan Addu’oi akan wannan tsari da
aka ambata guda hudu.
Mnnu//Ng0027
Ma'asumah Nigerian News Update