Bayan gama bukuwan aure, sai Manzon Allah (s) ya koma
gidan Khadijah da zama, wannan gida da ke da dimbin tarihi
wajen ci gabantar da musulunci da kuma taimakon marasa
galihu.
A yayin zamansu dai, Khadijah ta kasance mace mai tsananin
biyayya ga mijinta da kuma taimaka masa a dukkan bangarorin
rayuwarsa, kamar yadda shi ma ya kasance hakan tare da ita.
A lokacin da aka aiko shi a matsayin annabi, ita ce mace ta
farko da ta fara imani da shi, ta karbi wannan kira nasa, ta ba
da dukkan abin da ta mallaka don Allah da kuma ci gabantar
da wannan addini.
Babu makawa, dole ne Manzon Allah (s) ya saka mata saboda
irin wannan hidima da ta yi masa da kuma addinin Allah, don
haka ya kasance mai tsananin sonta, girmama ta lokacin tana
raye da ma bayan rasuwarta (a.s), daboda matsayin da take da
shi a cikin zuciyarsa.
An ruwaito cewa, bayan rasuwarta, a duk lokacin da ya yanka
wani abin yanka, ya kan dauki wani bangare na naman ya ce:
"Ku aika wannan wa kawayen Khadijah'. An ce wata rana
A'isha, matar Manzon Allah, ta tambaye shi me yasa yake
haka: sai ya ce mata: "Saboda ina sonta" .
Haka nan ma an ruwaito cewa wata mace ta zo wajen Manzon
Allah (s), a lokacin yana dakin A'isha. Nan take ya tashi ya
karbe ta hannu bibbiyu ya gaggauta biya mata bukatan da ta zo
nema. Wannan lamari ya ba wa A'isha mamaki, sai ta tambaye
shi dalilin hakan, sai ya ce mata: "Ta kasance tana zuwa
gurinmu lokacin rayuwar Khadijah".
Har ila yau kuma an ruwaito A'ishan dai tana cewa: 'Wata rana
Manzon Allah (s) zai fita daga gida, sai ya tuna da Khadijah, ya
fadi wasu kalmomi na girmamawa gare ta. To amma sai na
gagara rike kai na sai na ce masa; 'Ita dai ba wani abu ba ne
face tsohuwar mace, kuma a halin yanzu Allah ya musanya
maka wadanda suka fi ta'.
Nan take Manzon Allah (s) ya mayar mata da martani, cikin
fushi yana cewa: "Lallai ba haka ba ne...lalle ban samu
wadanda suka fi ta ba. Don kuwa ita ce ta yarda da annabcina
a lokacin da kowa ya kyale ni. Ta ba ni dukkan dukiyarta a
lokaci mafi tsanani (na bukatuwa da su). Kuma Allah Ya ba ni
zuriya ta hannunta, alhali kuwa ya haramta min daga wasunta".
Barka gare ki Ya Khadijah, barka gare ki Ya ke wacce Allah
Yake sonki kuma Ya kuma miki alkawarin dawwama cikin
ni'iman (aljanna). Don an ruwaito cewa Mala'ika Jibril (a.s) ya
zo wajen Manzon Allah (s) ya ce masa; "Ya Rasulallah! Ga
Khadijah nan za ta zo gurinka da kwarya na na abinci, idan ta
zo ka isar da gaisuwar Ubangijinta gare ta da kuma tawa
gaisuwar, ka kuma yi mata bushara da gida a aljanna da aka
gina shi da zinare....."
A saboda haka ne Manzon Allah (s) ya ce:
"Mafiya daukakan matan aljanna su ne: Khadijah bint
Khuwailid,Fatima bint Muhammad, Maryam bint Imran, Asiya
bint Muzahim, (matar Fir'auna)
Mnnu//Ng0027
Ma'asumah Nigerian News Update