Ma'anar Ibada


 


MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATE


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 



Bayan mutum yasan Ubangijinsa ta hanyar yin tunanin da ya kaishi ga fahimtar tushen samar da halitta baki ɗaya shine Allah , haka nan mutum yayi tunani akan kansa yaga cewa bashi da komai shima mabuƙaci ne a cikin komai dole ya koma ga Allah a cikin komai nashi , to anan ne ibada za ta tabbata kuma ma'anarta ; Sallamar mai tsananin buƙata zuwa ga Sakakken mawadaci mai karamci dan ya samu wani abu a wajensa .

Sannan anan ne ma'anar Addini take bayyana cewa shi wani ƙoƙo ne da mabuƙacin da bashi da komai yake amfani dashi wajen karɓa a wajen Mahaliccin da yake da komai , kuma wannan karɓar tana inganta ne idan shi mai karɓar bai kaucewa shiryarwar wannan ƙoƙon na karɓar muradinsa ba , yayin da mutum yake barin Allah ya tafi wajen wanin Allah , ma'anar hakan shine ya bar maɓuɓɓugar daddaɗan ruwa ya nufi wajen kawalwalniya da shirbici , kuma ya bar wanda yake da dukkan komai ya tafi zuwa ga wanda bashi da komai .


Daga nan za mu fahimci cewa ita Ibada bata inganta kuma bata tabbata sai idan ta kasance tsaftacciya ga Allah kaɗai .

Idan mai mai Azumi yayi niyyar yin Azumi saboda ya ya yardar da al'umar da yake rayuwa cikinsu ko don sabo duk shekara ana yi ko don jin kunyar sauran mutanen da yake rayuwa dasu ko saboda karin lafiya a jikinsa to Azuminsa ba zai taɓa zama karaɓabɓe ba .


Tabbas Wadannan abubuwane da mutum zai amfana dasu , sai dai basu bane asalin manufar yin Azumi ba sam , babbar manufar yin Azumi itace samun Taƙawa da kusanci ga Allah mabuwayi , Allah Ta'ala yana faɗa a cikin Alkur'ani :  

" Ya ku waɗanda kukayi imani an wajabta muku yin Azumi kamar yanda aka wajabtawa waɗanda suka gabaceku ko ku kwa sami Taƙawa " 


يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ (البقرة 183).


Shi yasa duk wanda bai samu Taƙawa da Azuminsa ba to Azuminsa bashi da wata ƙima kuma bai samu komai ba face ƙishirwa da yunwa , kamar yanda duk wanda Sallar da yake bata hana shi Alfahsha ba to babu wani abinda zai samu daga sallah face motsa jiki da yake yi .


Barkanmu da Buɗa baki 🌙


8/Ramadan/1444H - 30/3/2023 Miladiyya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post