Assalamu alaikum.
Sako na musamman zuwa ga yan'uwa Al-majiran malam zakzaky (H) na qasar Nigeria
Na lura da wani abu da za a gabatar a cikin Form da za a cika wajen kidayar Jama'a na qasa da za ayi.
Acikin tambayoyin da zasuma, zasu tambayeka.
Kai Musulmi ne?
Sannan wace aqida kake biya, idan kai Musulmi ne to ?
Sunna ne kai?
Shi'a ne kai?
Darika ne kai?
Duka dai sun saka wadannan tamboyoyi.
Abun lura anan!!
Akwai buqatar lallai dan'uwa yabasu amsa dacewa shi shi'a ne kuma mabiyi malan zakzaky (H).
Kada dan'uwa ko yar'uwa aji nauyin amsa wannan tambayar.
Saboda bamusan manufarsu ta saka wannan tambayar ba acikin wannan qidayar ba , ko ba komai akwai buqatar su san cewa, lallai Al-majiran malam zakzaky (H) sunada yawan da yakamata ace an sauraresu ta kowace janibi.
Haka ina bawa yan'uwa shawara da cewa subawa wannan qidayar da zasuyi muhimmancin gaske, wajen ganin kafito tare da yayanka da duk wadanda suke qar qashinka an kirga dasu.
Tare da natata cewa lallai dukanku Al-majiran malam zakzaky (H) ne.
Wannan sako ne dake da matukar muhimmancin gaske ga dukkanin yan'uwa Al-majiran malam zakzaky (H)
*Naziru sabaty Gusau ✍️*