Wannan Marubucin Mai Suna Abdullahi M Ali Ya Wallafa Rubutun sa ne A Shafin sa Na Facebook inda Yake Cewa"
" Ko Kasan Jagoran Harkar Musulunci A Najeriya Sheikh Ibraheem Yaqoub Al-Zakzaky (H) ya raba kayan abinci ga mabuƙata kamar yanda ya saba yi kowace shekara.
An raba kayan abincin ne ranar Laraba 29 ga watan Maris, 2022 Miladiyya. Kayan abincin da aka raba sun hada da shinkafa, Dawa, Masara, Gero da sauran su. A karshe Shehin Malamin yayi fatan alkairi ga dukkan al'ummar Musulmi.
Abin lura anan yawan cin masu cin amfani wannan Alkhairi ba Ƴan shi'a bane ko in ce Ƴar Harka Islamiya, A'a mutane gari Talakawa Mabuƙata su suka fi kowa cin amfanin wanna Alkhairin da Sheikh Zakzaky (H) ya daɗe yana yi tsawon shekaru, duk da ya kasance a cikin kurkuku a tsakanin shekaru 6, amma hakan bai sa ya fasa ba har zuwa fitowar sa a halin da ake yanzu.