Ummul Muminina Khadijah bint Khuwailid, matar Ma'aikin
Allah (s) ta rasu ne a ran 10 ga watan Ramalana shekara ta
goma da aiko Ma'aiki (s), wato shekara uku kenan kafin hijira,
a lokacin kuwa tana da shekaru 65 a duniya.
Kafin rasuwarta dai, Khadijah ta ba da gudummawa mai
girman gaske wajen kare Ma'aikin Allah (s) da kuma ci
gabantar da Musulunci a lokacin da yake cikin mawuyacin hali.
Saboda irin wannan gagarumar gudummawa da Nana Khadijan
ta bayar ne aka ruwaito Manzon Allah (s) yana cewa: 'Ba don
kariya ta Abu Talib ba, da kuma dukiyar Khadijah da kuma
takobin Ali ba, da wannan addini bai tsaya ba da kafarsa ba.
Wannan rasuwa ta Khadijah dai ya kasance babban rashi ga
Ma'aikin Allah da kuma 'yarsa Fatima (a.s) inda har tazo tana
kuka tana ce Baban nata (s) ina mahaifiyata, nan take sai
Mala'ika Jibril (a.s) ya sauko ya ce wa Annabi (s): "Ka ce wa
Fatima cewa Allah Madaukakin Sarki Ya gina wa mahaifiyarta
gida a aljanna da zinare...." .
Hakan kuma saboda irin wannan babban musiba da ta sami
Manzon Allah (s) na wannan rashi na Khadijah da kuma
rasuwar baffansa kuma mai kare shi Abu Talib (a.s), ya sa ya
kira wannan shekara (da suka rasu a cikinta) da "Shekarar
Bakin Ciki" .
Wace Ce Khadijah
To yanzu bari mu yi dubi kan wace ce Khadijah?
Ita ce dai Khadijah bint Khuwailid bn Asad bn Abdul Uzza bn
Qusay, tana daga cikin manyan matan Kuraishawa kana kuma
wacce ta fi su kyau, tun kafin Musulunci ma ana kiranta da
suna at-Tahira (tsarkakakkiya) saboda irin kyawawan dabi'unta,
kuma ana kiranta da 'Shugaban (matan) Kuraishawa.
Irin wadannan kyawawan halaye nata da kuma irin daukakan
da take da shi ya sa wasu daga cikin manyan Kuraishawa, irin
su Utbah bn Abi Mu'it, Abu Jahl, Abu Sufyan, da dai sauransu,
suka bukaci aurenta da kuma nuna mata kudi, to amma dai
taki ta zabi Manzon Allah (s) saboda halayensa na kwarai da ta
gani.
To kamar yadda muka fadi Khadijah mace ce mai dukiya, kana
kuma tana son wanda zai kula mata da wannan dukiya ta ta
cikin aminci ba tare da cuta ba, don haka sai ta bukaci Manzon
Allah (s), wanda daman tun zamanin Jahiliyya mutanen Makka
suna kiransa "As-Sadikul Amin, da ya kula mata da wannan
dukiya nata. Da farko dai ya ki yarda, to amma daga baya ya
amince da hakan.
Bayan wannan yarda da Manzon Allah (s) ya yi da wannan
bukata ta Khadijan, sai suka fita kasuwanci tare da wani bawan
Khadijan mai suna Maisara. A yayin wannan fatauci dai an
sami riba mai yawan gaske, hakan kuwa saboda albarkar da ke
tare da Ma'aikin ne da kuma gaskiyarsa. To bayan dawowarsu,
da kuma irin labarin da wannan bawa na Khadijah ya bata
dangane da irin kyawawan halaye na Manzon Allah (s) nan take
sai so da kaunarsa ta cika zuciyar Khadijah, inda ta bukaci in
ya yarda ya aure ta.
Mnnu//Ng0027
Ma'asumah Nigerian News Update