KASARNAN SAI TA ZAMA ISLAMIC REPUBLIC OF NIGERIA MAI BAKINCIKI SAI DAI KA MUTU




*Ma'asumah Nigerian News Update*


 *Tare da Bin Aliyu Daud (Dansudan)*


Cikin watan Azumi mai alfarma ake harbin Musulmai a Abuja, wannan wane irin zalunci ne, 'yansanda sun bude wuta haka kawai ga almajiran Sheak Ibraheem Zakzaky (H) a Abuja don sun fito, sun yi kira ga Gwamnati ta saki "passport din Shehin Malamin da ta rike, yaje neman lafiya, na harbin zaluncin da Gwamnatin ta yi masa shida matarsa harbin kisa a Zariya a 2015, bayan kashe duban mabiyansa. 

 Wannan zuba ido da mutane suka yi wasu har sunajin dadi, insha Allah Allah baya tare da azzalumi da wanda yake bayan azzalumi makomarsu wuta ne, kuma da sannu zaluncin azzalumin zai zo gareka, shirun da ka yi shi zai ja maka. Insha Allah da sannu za su girbi sakamakon zaluncinsu, haka kawai suna harbin mutanen da basu dauke da makami, wannan wane irin zalunci ne? Kuma a cikin wata mai alfarma, ana harbin Musulmai amman Musulmai sun yi gum da bakinsu, kawai magana suke suna fadin ayi adalci aka bude musu wuta, Allah yana gani dashi muka dogara kuyi ta zalunci insha Allah zai dauka mana fansa! Ranar daukan fansa tana zuwa kuci bashi iya san ranku za kuje lahira kuga sakamakon aikinku, Addinin Allah kuma kamar ya kafu ne a kasarnan, sai andawo ana hukunci da littafin Allah ba "constitution" ba. Sai ance Islamic Republic of Nigeria.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post